Ƙungiyar Tarayyar Afirka, AU ta ce ba ta so ta ɗaura wa Masar ko kuma wata ƙasa maƙwabciya laifi game da abin da ke faruwa a cikin ƙasar Ethiopia ba bayan Alƙahira ta ƙi yarda da wata sanarwar da ƙungiyar ta fara fitarwa game da rikice-rikicen yanki.
AU ta ce ta gane ƙin amincewar Masar ga sanarwarta ta ranar 1 ga watan Oktoba, wadda ta yi kira ga Ethiopia da Eritrea da kuma Masar su kai zuciya nesa sosai da barin ƙofofin tattaunawa a buɗe da sasanta matsalolinsu ta hanyar diflomasiyya.
“Babu wani yanayin da sanarwar ta yi niyyar ɗora alhakin abubuwan da ke faruwa a Ethiopia kan wata ƙasa maƙwabciya, in ji hukumar.
Ta ce kiran ya zo ne bayan an kori jami’an diflomasiyya daga Addis Ababa da Alkahira da Asmara kuma an yi shi ne domin hana rashin jituwa da taɓarɓarewar ko kuma faɗaɗa tashin hankali da zai iya barazana ga zaman lafiyar yankin.
Goyon bayan ‘yancin kan iyakoki
AU ta kuma sake tabbatar da jajircewarta ga ‘yancin kai da ‘yancin kan iyakoki da haɗin kan ƙasashe mambobinta tare da ƙa’idar rashin katsalandan a cikin harkokin cikin gidansu.
Ya jaddada cewa sanarwar ta faɗa ne kacokan cikin aikinta na inganta zaman lafiya da tsaro da lumana kuma ba ta da niyyar tsokaci kan ababen da ke faruwa a cikin ƙasashe mambobinta.
Masar ta ƙi amincewa ne da sanarwar hukumar ranar Asabar, inda wata majiya a hukumance ta bayyana ta a matsayin wani “yunƙuri da baza a iya ganewa ba” na shigar da Alkahira cikin wani lamarin cikin gida na Ethiopia.
Hukumar Ƙungiyar Tarayyar Afirka ta ce tana ba da muhimmanci na musamman ga dangantakarta da Masar, tana mai bayyana ƙasar a matsayin ɗaya daga cikin ƙasashen da suka kafa ƙungiyar da kuma wata muhimmiyar ƙawar aiki wajen inganta zaman lafiya da tsaro da haɗin kai da ci-gaba a faɗin Afirka.

















