| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
An zaɓi filayen wasa shida domin yin gasar AFCON ta 2027 a Gabashin Afirka
An zaɓi filayen wasa shida don gudanar da gasar AFCON ɗin ne a ƙasashen Kenya da Uganda da Tanzania.
An zaɓi filayen wasa shida domin yin gasar AFCON ta 2027 a Gabashin Afirka
Filan wasan Tunawa da Benjamin Mkapa a Dar es Salaam, Tanzania ɗaya ne daga cikin wuraren wasan shidan da aka zaɓa wa AFCON 2027. / CAFonline
 

An zaɓi filayen wasa shida domin gudanar da gasar Cin Kofin Afirka ta baɗi wadda ƙasashen Kenya da Tanzania da Uganda za su karɓi baƙuncinta.

Taron Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka da aka yi a ƙarshen mako a Nijeriya ne ya bayyana wuraren da za a yi wasan.

Babban birnin ƙasa na Nairobi shi kaɗai ne birni ɗaya tilo a Kenya da zai karɓi baƙuncin wasan a sabon filin wasa na Talanta mai iya ɗaukar mutum 60,000 wanda aka shirya buɗewa a watan Janairu.

Tanzania za ta kasance mai wuraren wasa uku a Arusha da Dar es Salaam da kuma Zanzibar.

Uganda za ta yi amfani da filin wasa na Ƙasa na Tunawa da Mandela a Kampala da kuma sabon filin wasan da aka gina na Hoima City, wanda Uganda ta yi amfani da shi don wasanninta na gida na kwanan baya.

Kawo yanzu dai ba a yanke shawara ba kan wuraren da za a buga wasanni 24 na ƙarshe na gasar, waɗanda za a yi tsakanin ranar 19 ga watan Yuni zuwa 17 ga watan Yulin 2027.

An buga wasannin gasar AFCON ta baya bayan nan ne a Maroko tsakanin watan Disambar 2025 zuwa watan Janairun 2026 a wurare tara a birane shida.