| Hausa
AFIRKA
3 minti karatu
Ghana za ta fara samar da allurar rigakafi a cikin gida nan da 2027
Ana shirin ne domin rage dogaron ƙasar kan rigakafin da ake shiga da su ƙasar daga ƙasashen waje da kuma gina masana’antar haɗa magununan ƙasar.
Ghana za ta fara samar da allurar rigakafi a cikin gida nan da 2027
Tsohon hoto: Shugaban Ghana yayin da yake gabatar da jawabi a taron zauren Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD) / AP (Wire)
 

Ana sa ran ƙasar Ghana za ta fara haɗa rigakafi na farko a cikin gida a farkon shekarar 2027 a wani ɓangare na ƙoƙarfin ƙarfafa haɗa rigakafi a cikin gida.

Kamfannin dillancin labaran ƙasar Ghana (GNA) ya ruiwato cewa ƙasar za ta fara ne da rigakafin tetenus da cutar mashaƙo da za a haɗa a cikin watanni huɗu na farkon shekarar 2027.

Ana shirin yin hakan ne domin rage dogaron ƙasar kan rigafin da ake shigowa da su cikin ƙasar da kuma gina masana’antar haɗa magununan ƙasar.

Shugaban Cibiyar Bincike Rigakafi na ƙasar (NVI), Dr Sodzi Sodzi-Tettey, ne ya bayyana wannan ranar Laraba a wajen buɗe ɗakin bincike da wuraren haɗa rigakafi a Cibiyar Binciken Lafiya na tunawa da Noguchi a babban birnin ƙasar, Accra.

Ya ce shirye-shiryen haɗa rigakafin na ta tafiya ba tare da tsayawa ba inda tuni abubuwa uku masu yawa da ake buƙata wajen haɗa rigakafin suka kasance a cikin ƙasar.

Abubuwan da aka haɗa a Indonesia a ƙarƙashin wata yarjejeniyar da ma’aikatar lafiyar ƙasar ta shiga, suna cikin harabar kamfanin haɗa magunguna na Atlantic Life Sciences, in ji shi.

Masu AlakaTRT Afrika - Hukumar Lafiyar Ghana: Larduna shida na fuskantar barazanar sanƙarau yayin da hunturu ke ƙaratowa

Dr Sodzi-Tettey ya ce ana tsammanin tsarin ya rage kuɗin haɗa magani da kuma ƙara sauƙi ga gwamnati.

Ya ce saya da kafa kayayyakin aiki tare da horas da masana kimiyya masu aiki a sabon ɗakin gwaje-gwajen wani lamari ne da gwamnati ta biya kuɗinsa gabaɗaya.

Cibiyar ta NVI tana kuma haɗa gwiwa da Cibiyar Hana Yaɗuwar Cututtuka ta Afirka (Africa CDC) da Kuma Cibiyar Ƙasa da Ƙasa ta Rigakafi don haɗa harkokin binciken Ghana da sauran cibiyoyin bincike irinsa a faɗin Afirka.

Dr Sodzi-Tettey ya ce manufar Ghana ta Haɗa magunguna da aka rattaɓa wa hannu kwnana nan na ba da ƙwarin gwiwa na ƙarfafa ƙarfin iya haɗa magunguna a cikin gida da kuma toshe giɓin ƙwarewa a masana’antar.

Ya yi ishara ga yafe haraji da aka yin kan abubuwa masu yawa na haɗa rigakafin tetanus-mashaƙo a matsayin ɗaya daga cikin matakai na manufa na tallafa wa haɗa rigakafin a cikin gida.

Shugaban cibiyar ya ce NVI, da haɗin gwiwa shirin samar da ƙwarewa ta haɗa magunguna, za ta kafa Hadakar Horaswa na Haɗa magungunwa zuwa ƙarshen shekarar 2027 domin tallaf wa horas da masana kimiyya da ƙwararru a masan’antar.

Ya ce haɗakar wadda za ta haɗa da makarantu da abokan aiki na masana’anta za ta samar da ƙwarewa na musmaman a muhimman fannoni da ake buƙata wajen taimaka wa sauya Ghana daga matakin saka rigakafi a cikin kwalabe zuwa matakin haɗa rigakafin daga farko zuwa ƙarshe.

Dr Sodzi-Tettey ya ce ministan lafiyar ƙasar ya kammala shirya takardar neman izinin alƙawurran sayayya a kasuwar nan gaba da kuma yarjejeniyar sayayya na shekara 10 domin tallafa wa haɗa rigakafi a cikin gida.

Ya ce Ghana za ta buƙaci aƙalla dala miliyan US$50 a ko wace shekara wajen siyan rigakafi bayan ta kauce wa tsare-tsaren tallafi na ƙetare kuma ya ce ya kamata a yi amfani da wani ɓangare na wannan kuɗin wajen ƙarfafa ikon iya samar da rigakafin a cikin gida.

“Muna buƙatar yin tunani bisa samar da wani asusu da zai tabbatar wa masa’antar cewa ba wai kawai muna ɗaukar alƙawarin saya ba ne, amma muna da kuɗin da za mu iya ci gabada saya da shi,” in ji shi.

Dr Sodzi-Tettey ya ce tsare-tsaren za su taimaka wajen riƙe zuba jari a acikin ƙasar da samar da ayyukan yi da kuma samar da wata kasuwa mai ɗorewa ta rigakafin da aka haɗa a cikin gida.