| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Tawagar Majalisar Dokokin Amurka ta isa Nijeriya, ta tattauna da Nuhu Ribadu
Babban Mai Bai wa Shugaban Nijeriya Shawara kan Tsaro, Nuhu Ribadu ya ce tawagar ta je Nijeriya ne domin tattara bayanai bayan tattaunawar diflomasiyya da tawagar Nijeriya ta yi a Washington a kwanakin baya kan zargin tauye haƙƙin addini.
Tawagar Majalisar Dokokin Amurka ta isa Nijeriya, ta tattauna da Nuhu Ribadu
Tawagar ta haɗa da ’yan majalisar wakilai na Amurka kamar su Mario Díaz-Balart, Norma Torres, Scott Franklin, Juan Ciscomani, da Riley Moore. / TRT Afrika Hausa
11 awanni baya

Wani kwamiti na Majalisar Dokokin Amurka ya isa Abuja kuma ya gana da Mai Ba wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaron Ƙasa, Nuhu Ribadu, yayin da ƙasashen biyu ke ƙara matsa ƙaimi wajen tattaunawar diflomasiyya kan haɗin gwiwar tsaro da kuma ƙaruwar damuwa a Washington game da zargin tauye haƙƙin addini.

Ribadu ya tabbatar da ziyarar ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, yana mai cewa ya karɓi tawagar ta “rangadin tattara bayanai a Nijeriya,” bayan wasu jerin tattaunawa da aka gudanar a Washington, D.C. kan muhimman batutuwan tsaro da ƙasashen biyu ke da su tare.

Tawagar ta haɗa da ’yan majalisar wakilai na Amurka kamar su Mario Díaz-Balart, Norma Torres, Scott Franklin, Juan Ciscomani, da Riley Moore.

Jakadan Amurka a Nijeriya, Richard Mills, shi ma ya halarci ganawar, wanda hakan ke muhimmancin wannan tattaunawar ga ƙasasehn biyu, kamar yadda Ribadu ya bayyana.

A cewar Ribadu, tattaunawar ta mayar da hankali kan yaƙi da ta’addanci, tabbatar da zaman lafiyar yanki da kuma ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka.

“Ina da kwarin gwiwa cewa wannan tattaunawa za ta ƙara amana, haɗin kai, da kuma jajircewarmu wajen samar da zaman lafiya da tsaro,” in ji Ribadu.

Tattaunawar ta ranar Lahadi na zuwa ne makonni bayan Mista Ribadu ya jagoranci wata babbar tawagar Nijeriya zuwa Washington, a lokacin da ake ƙara duba batun Nijeriya a Majalisar Dokokin Amurka tare da ƙoƙarin wasu ’yan majalisa na mayar da Nijeriya cikin jerin "Ƙasashen da ake damuwa da su matuƙa" saboda zargin cin zarafin Kiristoci.