Shugaban taro kan sauyin yanayi na COP31 Murat Kurum ya rufe taron na Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD) a Antalya ranar Lahadi ba tare da cim ma wata matsaya ba, yana mai sukar ƙasashe bisa gazawa wajen nuna sassauci da kuma jajircewar da ake buƙata don cim ma matsaya ta bai-ɗaya.
Kurum, wanda shi ne Ministan Muhalli da Birane da Sauyin Yanayi na Turkiyya, ya bayyana cewa ba a yanke shawara mai muhimmanci da aka shirya amincewa a kanta ba kafin a kawo ƙarshen taron na makonni biyu ta hanyar mataki na buga gudumar shari’a ba.
"Abin takaici ne wasu ƙasashe sun gaza nuna ƙoƙari da sassaucin da wannan nauyi mai cike da tarihi ke buƙata," kamar yadda Kurum ya bayyana a lokacin rufe taron.
"Mun gane muhimmancin abubuwan da ƙasaseh suka fi buƙata kuma muna girmama yanayi na ko wace ƙasa. Sai dai kuma, a kan irin wannan muhimmin batu game da makomarmu gaba ɗaya, za mu so dukkan ɓangarorin su ɗauki ƙarin nauyi wajen neman mafita," in ji shi.
Dangatakar za ta zarce rashin daidaito na taron COP31
Kurum ya ce Turkiyya ta ƙarƙare dukkan wani mataki mai yiwuwa don samar da matsaya ta bai-ɗaya a cikin dukkan tattaunawar, yana mai jaddada cewa matsalar ta sauyin yanayi ba za ta jira a warware rashin jituwa na diflomasiyya ba.
"Duniya ba ta jira, bala’o’i ba sa jira kuma mutane masu zuwa a gaba ba sa jira," in ji shi.
Ya kuma yi ishara ga ajandar matakan taron da dangataka ta ƙasashe da shirye-shiryen haɗin kai a matsayin nasarori masu ɗorewa da aka cim ma duk da gazawa wajen yanke shawarar kan babban mataki.
"Ina mai barin abin da ya faru a nan, yarjejejniyoyin da suka ci tura da kuma hanyoyin da aka bi zuwa wajen ga hukuncin duniya gabaɗaya da ma ɗaukacin bil Adama," kamar yadda Kurum ya bayyana.
Kafin ya buga gudumar shari’a ta rufe taro, ya gode wa tawagogin da suka halarci taron da takwarorinsa na Australia da kuma sakatareiyar MƊD bisa gudumowar da suka bayar.
"Gudumar da zan buga zai rufe wannan taron, amma ƙoƙarinmu zai ci gaba ," kamar yadda ya bayyana, inda ya rufe taron COP31 da CMP21 da CMA8 a hukumance.
Taron yanayin ya haɗa wakilan ƙasashe 196 da Tarayyar Turai a Antalya, Turkiyya, na tsawon makonni biyu don tattaunawa kan yanayi.














