| hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
INEC ta ayyana Charles Soludo na APGA a matsayin wanda ya lashe zaɓen Gwamnan Anambra
Charles Chukwuma Soludu ya samu nasarar samun wa'adi na biyu bayan ya samu ƙuri’u 422,664, yayin da Nicholas Ukachukwu na Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya biyo baya da ƙuri’u 99,445.
INEC ta ayyana Charles Soludo na APGA a matsayin wanda ya lashe zaɓen Gwamnan Anambra
Charles Soludo dai ya kasance tsohon gwamnan Babban Bankin Nijeriya CBN daga 2004 zuwa 2009
9 Nuwamba 2025

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana Charles Chukwuma Soludo na Jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna da aka gudanar a ranar 8 ga Nuwamba a jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Nijeriya.

Farfesa Edoma Omoregie, wanda shi ne babban bautren zaɓe na jihar ne ya sanar da sakamakon a cibiyar tattara sakamakon ta INEC da ke Awka, babban birnin jihar, da safiyar Lahadi.

A cewar sakamakon, Soludo ya samu ƙuri’u 422,664, yayin da Nicholas Ukachukwu na Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya biyo baya da ƙuri’u 99,445.

Paul Chukwuma na Jam’iyyar Young Progressives Party (YPP) ne ya zo na uku a zaɓen da ƙuri’u 37,753.

George Moghalu na Jam’iyyar Labour Party (LP) ne ya zo na huɗu da ƙuri’u 10,576, yayin da Jude Ezenwafor na Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya samu ƙuri’u 1,401.

Wannan sakamakon ya bai wa Soludo sabon wa’adin shekaru huɗu a gidan gwamnati na Light House da ke Awka.

Jam’iyyu goma sha shida da ‘yan takararsu ne suka fafata a zaɓen kujerar gwamnan Anambra.

Baya ga Soludo da Ukachukwu, sauran sun haɗa da John Nwosu na Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC).

Charles Soludo dai ya kasance tsohon gwamnan Babban Bankin Nijeriya CBN daga 2004 zuwa 2009 sannan ya zama gwamnan Anambra a shekarar 2022.

 

Rumbun Labarai
‘Yan wasan Super Eagles sun ƙaurace wa atisaye kan rashin biyansu alawus
Jiragen yaƙin Nijeriya sun kashe ‘yan ta’addan ISWAP da ɓarayin daji a Borno da wasu jihohin Arewa
Babu abin da za mu rasa idan Nijeriya ta daina hulɗa da Amurka – Sheikh Gumi
Damuwa kan kutsawar 'yan bindiga Jihar Kano
Rundunar sojin Nijeriya ta ce ta kuɓutar da mutum 86 da Boko Haram ta yi garkuwa da su
Gwamnatin Nijeriya ta amince a ci bashin dala 396 domin inganta kiwon lafiya da ayyukan jinƙai
An gabatar da kudiri a Majalisar Dokokin Amurka don saka wa Ƙungiyoyin Miyetti Allah takunkumi
‘Kisan kiyashi ga Kiristoci: Me ya sa kurarin Trump a Nijeriya yake kan kuskure da rashin dacewa?
Majalisar Dattawan Nijeriya ta amince a ɗaure malaman makaranta shekara 14 kan cin zarafin ɗalibai
An kashe 'yan ta'adda fiye da 592 a Borno tun daga Maris din 2025 - Ministan Yada Labaran Nijeriya
ECOWAS ta yi tir da ikirarin ‘ƙarya mai hatsari’ na Amurka cewa Nijeriya ta bari ana kashe Kiristoci
Hukumar DSS a Nijeriya ta kori ma'aikatanta fiye da 100
Amurka na da ajanda a Nijeriya tana fakewa da kisan Kiristoci - Sheik Bala Lau
China na adawa da Trump kan amfani da 'addini da ‘yancin ɗan'adam' domin tsoma baki a Nijeriya
Naira da hannayen-jari Nijeriya sun faɗi sakamakon barazanar da Trump ya yi ta kai hari ƙasar
Jami'an tsaron Nijeriya sun hallaka 'yan bindiga 19 a Jihar Kano
Yadda barazanar da Trump ya yi kan aika sojoji Nijeriya ta tayar da ƙura
Dakarun Nijeriya sun kuɓutar da mutanen da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su Jihar Kogi
Ya kamata Amurka ta taimaka wa Nijeriya da makamai maimakon barazana —Kwankwaso
Muna shirin ɗaukar mataki kan Nijeriya - Sakataren Ma’aikatar Yaƙi na Amurka