Shirye-shirye sun fara kankama yayin da ya rage ‘yan makonni a fara gasar kofin ƙasashen Afirka ta AFCON 2025, wadda hukumar ƙwallon ƙafar Afirka, CAF ke shiryawa.
Gasar za ta gudana ne tsakanin 21 ga Disamban 2025 zuwa 18 ga Janairun 2026 a ƙasar Marocco.
Tuni tarin ‘yanƙwallon Afirka da ke taka leda a wajen nahiyar suka fara haɗa kayansu don komawa gida su yi shirin buga gasar da ake yi duk bayan shekara biyu.
A ɓangaren ƙungiyoyin da za su rasa ‘yanwasa sakamakon gasar tsawon wata guda, akwai Liverpool, wadda za ta rasa ɗan wasa ɗaya tilo.
Gwarzon ɗanwasa ɗan asalin Masar, Mohamed Salah zai bar ƙungiyar don haɗuwa da tawagar ƙasarsa ta Pharaohs.
Sai dai a cewar kocin Liverpool, Arne Slot, ƙungiyar ba za ta yi saurin sakin ɗanwasan ya tafi wakiltar ƙasarsa ba, har sai ranar ƙarshe da dokar FIFA ta ce dole ya tafi.
Wasa da Nijeriya
Slot ya bayyana cewa ƙungiyar ta tattauna da Salah, da kuma hukumar ƙwallon Masar don tsayar da ranar tafiyar Mohamed Salah.
An yi ta samun jita-jitar cewa Salah zai bar Liverpool kafin lokacin da aka tsara, musamman ganin ba a sa shi a wasan makon jiya da Liverpool ta doke West Ham ba.
Dalili na biyu shi ne tawagar Masar ta shirya buga wasan sada-zumunta da tawagar Nijeriya ranar 14 ga Disamba.
Slot ya ce ranar da aka tsayar don tafiyar Salah ita ce 15 ga Disamba, kwana shida gabanin ƙaddamar da gasar. Ke nan Salah ba zai buga wasa da Nijeriya ba.
Hakan na nufin ɗanwasan zai halarci wasannin da Liverpool za ta buga da Sunderland, da Leeds, da Brighton a Gasar Firimiya.
Sannan zai samu damar buga wa Liverpool wasan Gasar Zakarun Turai tare da Inter Milan ranar 9 ga Disamba a Italiya.











