Rundunar Operation Hadi Kai da ke yaƙi da ‘yan ta’addan Boko Haram a arewa maso gabashin Nijeriya ta ce ta kuɓutar da mutum 86 da aka yi garkuwa da su tare da daƙile harin ‘yan Boko Haram.
A wata sanarwar da ta fitar ranar Lahadi, rundunar ta ce lamarin ya auku ne ranar 9 ga watan Nuwamba a Jihar Borno bayan dakarun sun samu labarin cewa mayaƙan Boko Haram suna kama mutane da motaci a kan hanyar Buratai zuwa Kamuye.
Da dakarun operation Hadin Kai suka samu labarin, sai suka yi ta kan ‘yan ta’addan a inda suke a hanyar Mangari inda mayaƙan suka tsere a gigice.
“Binciken da aka yi a yankin ya gano matsugunan wucin-gadi na ‘yan ta’adda sannan an kuɓutar da mutum 86 da aka yi garkuwa da su ciki har da maza da mata da ƙananan yara,” in ji sanarwar da Sani Uba, mai magana da yawun rundunar Operation Hadin Kai ya sanya wa hannu.
“Ababen da aka ƙwace sun haɗa da bindiga ƙirar AK-47 ɗaya da gidajen harsasai biyar da harsasai 73 da jidiga huɗu da motocin fararen-hula biyar da babura biyar da kuma babur mai ƙafa uku guda biyu,” in ji sanarwa.
Kazalika sanarwa ta ce sojojin sun lalata sansanin ‘yan ta’addan.
A wani labarin makamancin haka kuma, sanarwar ta ce sojojin da aka tura Mangada sun kama mutum 29 da ke taimaka wa ‘yan ta’adda da abubuwan amfanin yau da kullum a kan hanyarsu ta zuwa Chilaria da wasu kayayyaki.
“Kayayyakin da aka ƙwace a hannunsu sun haɗa da a-kori-kura biyu da babur mai ƙafa uku ɗaya da ke ɗauke da man fetur da ya kai kimanin lita 1,000a cikin jarka da galan huɗu na baƙin mai da sabbin tayoyin motar mai bindiga da tarin magunguna da kuma abinci mai yawa,” a cewar sanarwar.
Ta ƙara da cewa an kammala ayyukan ba tare da wani soja ya ji ciwo ba, lamarin da ya sa manyan sojoji suka yaba da irin bajintar da sojojin Operation Hadin Kai suke nunawa a arewa maso gabashin Nijeriya.


















