Sama da masu tseren sassarfa 41,000 daga ƙasashe 126 sun shiga gasar Tsere Sassarfa ta Istanbul, wato Türkiye İs Bankası karo na 47 ranar Lahadi, wadda ita ce gasar ɗaya tilo da da ake tsallakawa daga nahiyoyar Turai zuwa nahiyar Asiya.
Gasar Spor İstanbul ne suka shirya ta, kuma tana jerin gasannin tsere masu ajin zinare wajen hukumar wasannin motsa-jiki ta World Athletics.
Ta haɗa jimillar mutane 41,416. Gasara ta haɗo masu tsere 5,976 na kilomita 42, da masu tsere 12,440 a matakin kilomita 15.5, da masu tsere 18,000 a gasar gudun kamfanoni, da masu tsere 5,000 a na gudun gamagarin mutane.
Hanayr da aka bi tafara daga ɓangaren nahiyar Asiya na birnin Istanbul, mita 250 daga gadar Shahidan 15 ga Yuli, kuma ta ƙare a dandalin Sultanahmet Square a ɓangaren Turai European na birnin.
Gasar maza
Rhonzas Lokitam Kilimo ɗan Kenya shi ya lashe gasar maza, bayan gudun kilomita 42.195-cikin awa 2 da minti minti 10 da sakan 12.
Wanda ya lashe gasar bara, Dejene Debela ɗan Kenya, shi ya zo na biyu bayan gudun awa 2 da minti 10 da sakan 23, inda Sufaro Woliyi ɗan Ethiopia ya zo na uku da gudun awa 2 da minti 10 da kasan 26.
Gasar mata
Bizuager Aderra ‘yar Ethiopia ita ce ta lashe gasar mata da gudun awa 2 da minti 26 da sakan 19, sai mai bi mata Sofia Assefa ita ma ‘yar Ethiopia da gudun awa 2 da minti 26 da sakan 21. Joan Jepkosgei ‘yar Kenya ce ta uku, da awa 2 da minti 26 da sakan 36.
Gasar da ake duk shekara ta haɗo dubban masu tsere ƙwararru da waɗanda ba ƙwararru ba, wadda ya sanya gasar ƙayatarwa.
Waɗanda suka yi nasa zun samu kyautar dala $50,000, na biyu sun samu dala $20,000, na uku dala $10,000, inda na huɗu zuwa na takwas suka samu dala $1,000.






