Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce ya yi amfani da jawabinsa na 16 a Babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD) wajen kira ga samar da tsarin duniya da ya fi adalci da kuma sake tabbatar da goyon bayan Turkiyya ga Falasɗinu.
“Za mu ci gaba da magana cikin jarunta ga abin da ya dace da kuma bayyana gaskiya,” kamar yadda Erdogan ya bayyana bayan wani zaman majalisar ministoci a Ankara ranar Litinin.
Da yake tuna kan irin rawar da ya taka a Babban Zauren MƊD na 81 a New York, Erdogan ya ce ya gabatar da wani tsari mai manufofi biyar na sabon tsarin duniya bisa ƙarin adalci da ƙarfafa wakilci da aminci da kuma wadata.
Ya kuma zayyana matsayar Turkiyya kan Gaza da kuma Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye da yaƙin Rasha da Ukraine da kuma tashin hankalin da ya shafi Iran.
‘Ba za mu ja da baya ba’
Erdogan ya ce “ta’addancin” Isra’ila a Gaza da kuma Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye shi ne Turkiyya ta fi mayar da hankali a kai a harkokin ƙasa da ƙasa.
Ya soki rashin bai wa Shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas damar halartar Babban Taron, yana mai cewa ƙuntatawa wajen ba da biza ce ta hana shi kasancewa a wurin da kansa.

“Yayin da masu aikata laifukan yaƙi waɗanda kalamansu ke warin jini suka samu wuri a kan dandamalin MƊD domin yaɗa ƙarairayinsu, kasancewa Shugaba Abbas bai iya zuwa wurin ba abin kunya ne ga bil’adama,” in ji Erdogan.
Ya ce Turkiyya za ta ci gaba da tallafa wa Falasɗinawa da ‘yan Lebanon da rikicin ya shafa.
“Ba za mu taɓa yin watsi da matsayarmu ba har sai an gurfanar da waɗanda suka aikata laifuka kan bil’adama a gaban kotu, waɗanda suka zubar da jinin ‘yan’uwanmu maza da mata 74,000 a Gaza, waɗanda suka yaɗa ta’addanci a faɗin yankinmu daga Lebanon zuwa Syria,” in ji shi.
Tuntuɓa ta diflomasiyya da tattalin arziki
Erdogan ya ce ya yi wasu ganawa na dangantaka da shuwagabannin ƙasashe da na gwamnatocin ƙasashe 17 a lokacin ziyararsa a New York kuma ya halarci wani zama na haɗin kan Amurka da ƙungiyar ƙasashen yankin Gulf bisa gayyatar Trump.
“Bisa gayyatar Mista Trump, na halarci wani zaman da Amurka da ƙungiyar haɗin kan ƙasashen yankin Gulf, inda na bayyana ra’ayoyinmu kan dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin,” in ji shi.
Ya kuma gana da wakilan kamfanonin Amurka domin tattauna damarmaki na zuba jari a Turkiyya kuma ya halarci shirye-shirye da suka ƙunshi al’ummomin Turkiyya da Amurka da Musulmai.
Erdogan ya bayyana cibiyar Turkevi Center a New York a matsayin cibiyar diflomasiyya kuma ya tuna halartar bikin rufe baje-koli na ƙasa da ƙasa na 21 na MUSIAD EXPO da kuma Taron ‘Yan kasuwa na ƙasa da ƙasa ranar 26 ga watan Satumba.
Ya ce jerin tuntuɓar da ya yi a lokacin taron Babban Zauren MƊD za ta amfani Turkiyya da kuma al’ummomin da rikici ya shafa, yayin da yake bayyana fatan cewa tarukan za su yi silar sabbin haɗin gwiwa da haɗin kai.





















