| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
Remi Tinubu ta yi watsi da zargin tsayar da gwamnan Osun daga yin waka a taron nadin sarautarta
A wani saƙo da ta wallafa a shafinta na Facebook a ranar Talata, Remi Tinubu ta ce, ‘‘Masu suka sukan mayar da ƙaramin abu ya zama babba, kuma hakan na haifar da ruɗani a yanayin shugabanci.’’
Remi Tinubu ta yi watsi da zargin tsayar da gwamnan Osun daga yin waka a taron nadin sarautarta
Matar shugaban Nijeriya Remi Tinubu ta yi watsi da zargin dakatar da gwamnan Osun daga yin waka a taron nadin sarauta da aka ba ta / TRT Afrika
10 Disamba 2025

Matar shugaban ƙasar Nijeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta yi watsi da zargi da kuma sukar da jama’a ke yi mata kan tsayar da gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke daga yin waƙa a wurin wani taro, tana mai bayyana martanin da ‘‘tsegumi mara amfani’’.

A wani saƙo da ta wallafa a shafinta na Facebook ranar Talata, Remi Tinubu ta ce, ‘‘Masu suka sukan mayar da ƙaramin abu ya zama babba, kuma hakan na haifar da ruɗani a yanayin shugabanci.’’

Oluremi ta ƙara da cewa, "Waɗanda aka ba wa amanar shugabanci sun fahimci ayyukansu da kuma yadda za su jagoranci al'amuran da suka shafi al'umma.

"A mafi yawan lokuta, mabiya da masu suka ne suke yin ƙwaƙƙwafi kan kowane mataki, suna ƙara girman ƙananan kurakurai, sannan su mayar da su ce-ce-ku-ce maras amfani," a cewar saƙon matar Shugaban Nijeriyar.

Ta ƙarƙare kalaman nata ne da wani bidiyo na bikin cika shekara 10 na naɗin sarautar Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi, wanda ya nuna gwamna Adeleke ya dakata bayan wata gajeriyar waƙa da ya rera a yayin jawabinsa.

A bidiyon, an ga Remi Tinubu ta taho kan mimbarin taron, ta yi masa raɗa - yanayin da ya karaɗe kafofin sada zumunta, kuma ya jawo martani da suka a shafukan yanar gizo.

Kalaman matar shugaban Nijeriyar na yau, sun nuna martaninta farko ga ‘yanƙasar tun bayan da bidiyon ya yaɗu.

Duk da haka, lamarin ya haifar da muhawara mai zafi a shafukan sada zumunta, inda wasu 'yan Nijeriya ke cewa matar shugaban ƙasar ta wuce gona da iri, ganin yadda ta gwale Adeleke, wanda shi ne gwamnan jihar Osun na yanzu, a wurin bikin.

Gwamnan na Osun ya yi fice wajen rawa da waƙa a bainar jama'a, musamman idan ya halarci wuraren bukukuwa.

A ɓangare guda kuma, wasu sun kare matakin da Oluremi ta ɗauka, suna cewa gwamnan ya ɗauki lokaci mai tsawo yana waƙa, maimakon ya gabatar da jawabinsa.

Ko da yake dai, kawo yanzu gwamnan bai fito fili ya yi tsokaci game da lamarin ba.

A bikin na ranar Lahadi, 7 ga Disamban 2025, an ba wa matar shugaban Nijeriyar sarautar gargajiya ta yankin Yarabawa ta ‘Yeye Asiwaju Oodua’, wadda, a cewar Babban basaraken na ƙasar Yarabawa, Ooni na Ife, laƙabin sarautar na "nuna shugabanci, da hidima, da tausayi, da kuma jajircewa ga ci gaban al'ummar Yarabawa da ma Nijeriya baki ɗaya”.

Bikin ya samu halartar manyan mutane, ciki har da gwamnonin jihohi da dama, da tsohon shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo, da Sarkin Musulmin Nijeriya, Muhammadu Sa'ad Abubakar III.