| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Majalisar Dattijan Nijeriya ta amince da tura sojoji Jamhuriyar Benin
Bayan shugaba Bola Tinubu ya miƙa buƙatar neman amincewar majalisar, a zamanta na ranar Talata Majalisar Dattijan Nijeriya ta amince da tura sojojin wanzar da zaman lafiya zuwa Jamhuriyar Benin.
Majalisar Dattijan Nijeriya ta amince da tura sojoji Jamhuriyar Benin
Buƙatar girke sojojin a Benin na zuwa ne bayan wani yunkurin juyin mulki a ƙasar. / Nigerian Senate
9 Disamba 2025

Majalisar Dattijan Nijeriya ta amince wa shugaban ƙasar Bola Tinubu ya tura sojojin kiyaye zaman lafiya zuwa maƙwabciyarta Benin.

Tun da fari, shugaba Tinubu ya nemi amincewar majalisar bayan da aka yi yunƙurin juyin mulki a ƙasar da ke tare da Nijeriya cikin Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Ƙasashen Yammacin Afirka, ECOWAS.

Shugaban Majalisar Dattawan, Sanata Godswill Akpabio ne ya sanar da amincewar ranar Talatar nan bayan da ‘yan majalisar suka duba buƙatar shugaban Nijeriyar.

Sun yi wannan aiki ne ƙarƙashin dokar Sashe na 5, Babi na 11 na kundin tsarin mulkin Nijeriya.

Sanatocin sun amince a jumlace kan yarjewa a girke sojojin Nijeriya domin taimakawa zaman lafiyar yankin Yammacin Afirka.

Shugaba Akpabio ya kuma yi nuni da alhakin Nijeriya na tallafawa ƙawayanta na ECOWAS, inda ya ce za a aike da wasiƙar amincewar majalisa ga shugaba Tinubu nan-take.

Ceton dimokuraɗiyya

Yunƙurin juyin mulki da Nijeriya ta taimaka wajen hana yin nasararsa ya zo ne a ƙarshen makon da ya wuce, makonni bayan wani juyin mulkin a wata ƙasar mambar ECOWAS, wato Guinea-Bissau.

Sannan a shekarun baya-bayan nan, an samu irin sauyin shugabancin a wasu ƙasashe huɗu na ECOWAS, wato Nijar, Mali, Burkina Faso, da Guinea.

Tuni ƙasashe uku cikinsu, wato Nijar da Mali da Burkina Faso suka fice daga ECOWAS kuma suka kafa sabon ƙawancen ƙasashen Sahel mai suna AES.

Wannan lamura na ɗaukar hankalin duniya ganin cewa ECOWAS na ƙoƙarin ceton dimukuraɗiyya a Yammacin Afrika.