Fitattun mutanen da ke tsilla-tsilla gabanin zaɓen 2027
SIYASA
5 minti karatu
Fitattun mutanen da ke tsilla-tsilla gabanin zaɓen 2027Yayin da Nijeriya ke shirin babban zaɓen 2027, sauye-sauyen matsayar wasu fitattun mutane a fagen siyasa na ƙara jawo ce-ce-ku-ce, musamman a kafofin sada zumunta, inda ake tambayar gaskiyar akidarsu da dalilan da ke sa suke sauya goyon baya.
Nigeria Election / AP (Wire)
 

Yayin da siyasar Nijeriya ke ƙara ɗaukar zafi gabanin babban zaɓen 2027, wani yanayi da ke jan hankali shi ne sauye-sauyen matsayar wasu fitattun mutane waɗanda suka gina suna ta hanyar sukar gwamnati, iƙirarin kishin ƙasa da fafutukar kawo sauyi a shugabanci.

Wasu daga cikin waɗannan mutane, waɗanda a baya suka shahara wajen bayyana matsalolin ƙasar da kuma kira ga shugabanci na gari, yanzu ana ganin suna sauya alaƙarsu da manyan ɓangarorin siyasa. Wasu sun koma goyon bayan jam’iyya mai mulki ta APC, yayin da wasu kuma suka karkata zuwa ga ’yan adawa.

Wannan yanayi na tsilla-tsilla a siyasa, musamman tsakanin matasa da fitattun masu tasiri a kafofin sada zumunta, na ci gaba da jawo muhawara kan abin da ke motsa su wajen ɗaukar irin waɗannan matakai.

Daga fafutukar kawo sauyi zuwa siyasar jam'iyyu

A Nijeriya, wasu fitattun masu sharhi da fafutukar siyasa sun gina tasirinsu ne ta hanyar sukar manufofin gwamnati, fallasa matsalolin shugabanci da kuma kira ga sauye-sauyen da za su inganta rayuwar jama'a.

Daga cikin waɗanda suka yi fice wajen sharhi kan matsalolin shugabanci da tsaro a ƙasar akwai Bulama Bukarti, wanda ya sha yin kira ga inganta shugabanci da magance matsalolin da ke addabar Nijeriya.

Irin wannan fage na fafutuka da sharhi kan al'amuran ƙasa ya sa ake ƙara duba matsayin fitattun mutane a siyasa, musamman idan aka ga sauyin matsaya ko alaƙarsu da wasu ɓangarorin siyasa. Hakan na tayar da tambayoyi kan daidaiton akidarsu da kuma yadda suke bayyana dalilan matakan da suke ɗauka.

Firdausi Yahaya: Daga Atiku zuwa Tinubu

Ɗaya daga cikin misalan da suka jawo hankalin jama'a a kwanakin baya shi ne na fitacciyar jarumar fina-finan Hausa, Firdausi Yahaya, wadda ta sanar da komawa goyon bayan Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bayan ta ajiye aikinta a kwamitin yaƙin neman zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar.

Matakin nata ya haifar da muhawara a kafofin sada zumunta, inda wasu suka soki sauyin goyon bayan da ta yi, yayin da wasu ke ganin cewa tana da cikakken 'yancin zaɓar ɗan takara ko ɓangaren siyasar da take son mara wa baya.

Lamarin ya sake buɗe muhawarar kan rawar da fitattun mutane ke takawa a siyasa da kuma irin tasirin da matsayarsu ke yi ga magoya bayansu.

Moofy da Zee Gombe: Sauye-sauyen goyon baya a Gombe

A jihar Gombe ma, sauye-sauyen goyon bayan wasu fitattun mutane sun jawo ce-ce-ku-ce, musamman a tsakanin masu bibiyar harkokin siyasa a kafofin sada zumunta.

Mufida Adnan, wadda aka fi sani da Moofy, fitacciyar mawaƙiya ce da ta shafe lokaci tana tallata ɗan takarar gwamnan jihar Gombe na jam'iyyar PDP, Farfesa Isa Ali Pantami.

A shafukanta na sada zumunta, ta sha bayyana Pantami a matsayin ɗan takarar da ya fi cancanta ya jagoranci jihar. Sai dai a kwanakin baya ta koma goyon bayan ɗan takarar jam'iyyar APC, Dokta Jamilu Gwamna.

Wannan sauyin matsaya ya jawo tambayoyi daga wajen wasu masu bibiyarta, musamman ganin irin yadda a baya ta nuna cikakken goyon baya ga Pantami.

Ita ma fitacciyar 'yar TikTok, Zee Gombe, ta yi fice wajen tallata Pantami, kafin daga baya ta koma goyon bayan Jamilu Gwamna. Daga bisani kuma ta sake komawa wajen Pantami.

Sauye-sauyen da ta yi fiye da sau ɗaya sun jawo mamaki da muhawara, inda wasu ke tambayar ainihin matsayarta tsakanin manyan 'yan takarar biyu da ke neman kujerar gwamnan jihar.

Me ya sa sauya matsaya ke jawo ce-ce-ku-ce?

A wasu lokuta, mutane kan goyi bayan fitattun mutane ba kawai saboda shahararsu ba, har ma saboda akida da matsayin da suke ɗauka kan matsalolin da suka shafi al'umma.

Idan mutum ya gina sunansa a kan kare muradun talakawa, sukar gwamnati da fafutukar kawo sauyi, magoya bayansa kan fara kallonsa a matsayin wanda ke magana a madadinsu. A wasu lokutan, har sukan ɗauke shi a matsayin wakilin muradunsu a fagen siyasa.

Saboda haka, idan daga baya irin wannan mutum ya sauya matsayarsa ko ya koma goyon bayan tsarin da a baya yake suka, hakan kan haifar da tambayoyi kan gaskiyar akidarsa da kuma dalilan da suka sa ya sauya matsaya.

Wasu na ganin cewa irin waɗannan sauye-sauye na iya zama alamar fifita moriyar kai a kan muradun jama'a. A ganinsu, wasu na amfani da shahararsu da tasirin da suke da shi a tsakanin matasa wajen samun matsayi ko wata moriya ta siyasa.

Sai dai ba kowane sauyin ra'ayin siyasa ba ne ke nuna cin amana ko son abin duniya. Kowa yana da 'yancin sake nazarin matsayarsa, sauya ra'ayinsa da kuma zaɓar wanda yake ganin zai iya wakiltar muradunsa. Haka kuma, sauyin goyon bayan ɗan takara ba lallai ne ya zama sauya sheƙa daga wata jam'iyya zuwa wata ba.

Abin da ke da muhimmanci shi ne bayyana dalilan da suka haifar da sauyin matsayar, musamman idan mutum ya shafe lokaci yana jan hankalin jama'a kan wata akida ko matsayar siyasa.

A ƙarshe, yayin da Nijeriya ke tunkarar zaɓen 2027, sauye-sauyen da ake gani na iya ci gaba da zama abin tattaunawa a tsakanin jama'a. Babbar tambayar ita ce: shin waɗannan sauye-sauyen na nuna sauyin akida ne, ko kuwa akwai wasu muradu da ke bayan su?

Kuma a siyasance, har yaushe fitattun mutane za su iya riƙe amincewar jama'a idan matsayarsu ta ci gaba da sauyawa?