| Hausa
NIJERIYA
1 minti karatu
Aƙalla sojojin Nijeriya da Ivory Coast 200 sun isa Benin bayan an daƙile yunƙurin juyin mulki
Yunƙurin juyin mulkin ya girgiza Benin ranar Lahadi, lamarin da ya sa Nijeriya da Ivory Coast suka tattara dakaru domin tallafa wa gwamnatin na farar-hula.
Aƙalla sojojin Nijeriya da Ivory Coast 200 sun isa Benin bayan an daƙile yunƙurin juyin mulki
An murƙushe yunƙurin juyin mulkin da wasu sojoji suka nemi yi wa gwamnatin Shugaba Patrice Talon a Cotonou / Reuters
3 awanni baya

Sojojin Nijeriya da Ivory Coast 200 sun isa Jamhuriyar Benin a wani ɓangare na aikin tallafa wa gwamnatin ƙasar bayan yunƙurin juyin mulkin da aka yi a ƙasar a ƙarshen mako, kamar yadda ministan harkokin wajen ƙasar ya bayyana ranar Alhamis.

Yunƙurin juyin mulkin ya girgiza Benin ranar Lahadi, lamarin da ya sa Nijeriya da Ivory Coast suka tattara dakaru domin tallafa wa gwamnatin na farar-hula.

"A halin yanzu akwai misalin sojoji 200, waɗanda suka zo ba da tallafi wa dakarun tsaron Benin a wani ɓangare na aikin kawar da gyauron sojoji masy tayar da ƙayar baya," kamar yadda Olushegun Adjadi Bakari ya bayyana wa manema labarai a babban birnin Nijeriya.

Wata majiyar tsaron Ivory Coast ta bayyana cewa ƙasarsa ta tura dakaru hamsin a wani ɓangare na aikin, wanda ƙungiyar ECOWAS ta ce zai haɗa da sojoji daga Ghana da Saliyo.

Yunƙurin juyin mulkin ‘ya riga ya ci tura'

Nijeriya ta bayyana cewa sojojinta sun isa Benin ranar Lahadi.

Bakari ya ce zuwa lokacin da dakarun Benin suka nemi a tallafa musu, yunƙurin juyin mulkin "ya riga ya ci tura."