| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Sojojin Nijeriya sun daƙile harin ISWAP, sun lalata motocin ƙunar-baƙin-wake na 'yan ta'adda
'Yan ta’addan sun yi yunkurin kutsawa cikin sansanin soji na Mairari ta hanyar amfani da motocin ƙunar-baƙin-wake guda biyu. Sai dai sojojin da ke aikin sa ido sun gano tare da tarwatsa motocin kafin su kai ga shiga sansanin.
Sojojin Nijeriya sun daƙile harin ISWAP, sun lalata motocin ƙunar-baƙin-wake na 'yan ta'adda
A yayin wannan aiki, an gano karin gawawwakin ’yan ta’adda tare da kwato makamai, alburusai da kayan aiki da suka bari yayin tserewarsu. / Nigerian army
14 Disamba 2025

Sojojin Operation HADIN KAI (OPHK) sun yi nasarar dakile wani hari da ’yan ta’addar ISWAP suka kai kan sansanin soji a Mairari, lamarin da ya ƙara karya lagon ‘yan ta’addan da ke aikata laifuka a yankin.  

Harin ya fara ne a daren 12 ga Disamban 2025, ya kuma ci gaba zuwa safiyar 13 ga Disamba, inda sojoji suka mayar da martani cikin gaggawa ta hanyar hadin gwiwar dakarun ƙasa da na sama.

A yayin harin, ’yan ta’addan sun yi yunkurin kutsawa cikin sansanin ta hanyar amfani da motocin ƙunar-baƙin-wake guda biyu. Sai dai sojojin da ke aikin sa ido sun gano tare da tarwatsa motocin kafin su kai ga shiga sansanin.

Bidiyon CCTV da bayanan da aka samu daga filin daga sun tabbatar da cewa an kashe ’yan ta’adda da dama, yayin da wasu kuma suka samu munanan raunuka. Waɗanda suka tsira sun tsere suna kwashe gawawwaki da wadanda suka jikkata.

Bayan daƙile harin da ‘yan ta’addan suka yi yunƙurin kaiwa, sojojin OPHK na  tare da taimakon wasu dakaru na musamman waɗanda suka haɗa da ‘yan sanda da ‘yan bijilanti sun gudanar da bincike mai zurfi a yankin.

A yayin wannan aiki, an gano karin gawawwakin ’yan ta’adda tare da kwato makamai, alburusai da kayan aiki da suka bari yayin tserewarsu.

Abubuwan da aka kwato sun hada da bindigogin AK-47, jigidar alburusai, harsasan PKT, gurneti, babura, na’urorin sadarwa, kayan yaki, kayan jinya da sauran kayayyakin da ke nuna ci gaba da ayyukan ta’addanci.

Motocin bama-bamai guda biyu da aka dakile an tarwatsa su ta hanyar wutar kare kai ta sojoji, lamarin da ya haifar da lalacewa a wurare biyu a kan hanya. Muhimmin abu shi ne babu wata nasara da aka samu wajen kutsawa cikin sansanin, abin da ke nuna shirin ko-ta-kwana, sa ido da jajircewar sojoji.