| Hausa
NIJERIYA
1 minti karatu
Gwamnatin Nijeriya ta karɓo ɗalibai 100 da aka sace daga St. Mary’s Catholic School a Jihar Neja
'Yanbindiga sun kai hari a makarantar St. Mary’s Catholic School da ke Papiri a Jihar Neja ne ranar 21 ga watan Nuwamba inda suka sace mutum 315 — ɗalibai 303 da malamai 12.
Gwamnatin Nijeriya ta karɓo ɗalibai 100 da aka sace daga St. Mary’s Catholic School a Jihar Neja
A ranar 21 ga watan Nuwamban 2025, ‘yanbindiga sun kai hari a St. Mary’s Catholic School inda suka sace mutum 315 —ɗalibai 303 da malamai 12. / AP
8 Disamba 2025

Gwamnatin Nijeriya ta karɓo ɗalibai 100 cikin waɗanda aka sace daga makarantar St. Mary’s Private Catholic Primary and Secondary School da ke ta ƙauyen Papiri ƙaramar hukumar Agwara a Jihar Neja.

Kafofin watsa labaran Nijeriya ne suka ambato majiyoyin tsaro da hukumomin Nijeriya suna tabbatar da sakin ɗaliban ranar Lahadi.

A ranar 21 ga watan Nuwamban 2025, wasu ‘yanbindiga a kan babura sun kai hari a St. Mary’s Catholic School inda suka sace mutum 315 —ɗalibai 303 da malamai 12.

Jami’an tsaro da mafarauta sun fantsama cikin dajin yankin inda suka yi ta neman mutanen da aka sace.

Daga bisani, hukumomin makarantar sun ce ɗalibai aƙalla 50 sun tsere daga masu garkuwa da mutanen inda suka koma wurin iyayensu.

Hakan na nufin akwai mutum 265 a hannun ɓarayin dajin— ɗalibai 253 da kuma dukkan malamansu 12.

Lamarin ya tayar da hankalin gwamnatin Nijeriya da ma al’ummar ƙasar, har ta kai ga gwamnonin wasu jihohin arewacin ƙasar, ciki har da Jihar Neja, suka bayar da umarnin rufe wasu makarantu domin kauce wa sace ƙarin ɗalibai.