Umarnin da sojojin Sudan ta Kudu suka bayar na a fice daga garin Akobo da ke hannun ‘yan adawa a farkon wannan watan ya tilasta wa aƙalla mutane 100,000 tserewa ta kan iyaka zuwa Habasha, a cewar hukumar UNICEF a ranar Talata.
Akobo da ke yankin gabashin jihar Jonglei ya zama wuri na baya bayan nan da ake yawan samun rikici, yayin da a ɓangare guda faɗa tsakanin gwamnati da 'yan adawa ya tilasta wa Sudan ta Kudu shiga yaƙin basasa.
Tun daga ranar 6 ga watan Maris, rundunar sojin ta ba da umarnin kwashe mutanen daga garin, ciki har da jami’an hukumomin agaji na ƙasashen waje.
Ta ce tun daga lokacin ta ƙwace iko da Akobo, duk da cewa an samu bayanai da suka ci karo da juna game da abubuwan da suka faru, waɗanda ba a iya tantance su ba saboda ƙarancin hanyoyin sadarwa.
Wata majiyar tsaro ta shaida wa AFP cewa sojoji sun ƙwace barikin sojoji a Akobo kuma sun lalata gine-gine a kusa da wurin don samar da yankin tsaro, amma har yanzu ba a fitar da wani rahoto ba a hukumance.
Sata a asibiti
Hukumar kula da yara ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce "tashin hankali da rikici suna ƙara muni" a faɗin Jonglei, lamarin da ke ‘‘dagula yanayin da yara suke ciki.’’
"Aƙalla mutane 100,000 ne suka tsallaka iyaka zuwa Habasha, wasu kuma sun koma yankuna mafi aminci a jihohin Jonglei da Upper Nile," kamar yadda UNICEF ta bayyana a cikin wata sanarwa.
"Dukka waɗanda ke karɓar magani a asibitin Akobo - wanda a baya ya kasance wurin mafaka ga marasa lafiya da waɗanda suka ji rauni - sun tafi. Rahotanni sun tabbatar da cewa an yi ta sata a sibitin kuma yanzu an rufe shi."
Kazalika an bayyana cewa, adadin yara da ke fama da rashin abinci mai gina jiki ya ‘‘ƙara yawa sosai’’.
An lalata cibiyoyin kiwon lafiya da na samar da abinci mai gina jiki guda 28 a Jonglei a cikin wannan shekarar, a daidai lokacin da yankin ke fama da ɓarkewar cutar kwalara, in ji hukumar.
Tun a shekarar 2011 Sudan ta Kudu ta samu 'yancin kai, sai dai ba ta jima ba ta faɗa cikin yaƙin basasa kuma har yanzu tana fama da tsananin talauci da cin hanci da rashawa.
A farkon shekarar 2025 batun yarjejeniyar raba iko ta shekarar 2018 tsakanin Shugaba Salva Kiir da ɗadadden abokin hamayyarsa Riek Machar take tarɓaɓarewa, inda faɗa ya ɓarke a yankuna da dama kuma ya haifar da fargabar komawar ƙasar ga yaƙin basasa.












