| Hausa
WASANNI
1 minti karatu
Ronaldo ya zuba jari a Perplexity, kamfanin AI mai bin sahun ChatGPT
Cristiano Ronaldo ya faɗaɗa kasuwancinsa ta hanyar zuba jari a kamfanin ƙirƙirarriyar basira na Perplexity wanda ke bin sahun ChatGPT.
Ronaldo ya zuba jari a Perplexity, kamfanin AI mai bin sahun ChatGPT
Cristiano Ronaldo na fatan kafa sabon tarihin halartar gasar Kofin Duniya ta 2026 / AP
10 awanni baya

Gwarzon ɗanƙwallon ƙafa ɗan asalin Portugal, Cristiano Ronaldo ya zuba jari a sanannen kamfanin ƙirƙirarriyar basira na Perplexity.

Shafin kamfanin shi ke biye wa shafin ChatGPT a farin jini, sakamakon yadda yake haɓaka har yake neman kamo ChatGPT.

Labarin zuba jarin da ɗanwasan da a yanzu yake taka leda a Al Nassr ta Saudiyya ya yi, ya zo ne cikin wata sanarwar bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta.

Wani ɓangare na jarin ya ƙunshi cewa Ronaldo zai zama jakadan kamfanin da aka kafa a 2022, da zummar inganta burin kamfanin na samun fifiko a faɗin duniya.

Wannan mataki na ɗanwasan mai shekaru 41 na nuni da yadda yake faɗaɗa dabarunsa na kasuwanci, wadda ya ƙunshi harkokin motsa-jiki, marabci, da ayyukan fasaha.

A halin yanzu, kamfanin Perplexity yana da kimar dala biliyan $20.

A baya-bayan nan, an ambato Ronaldo yana cewa ya yi amfani da shafin Perplexity don shirya jawabinsa, inda tun a lokacin aka yi tunanin suna da alaƙa.

Shafin na ƙirƙirarriyar basira ya yi suna wajen amsa tambayoyin masu amfani da shi, da kuma ƙirƙirar abubuwan da ake iya nunawa a allon kwamfuta ko waya.