Rawar da Turkiyya ke takawa cikin tsare-tsaren tsaron da Turai ke jagoranta, ciki har da shirin tsaron Turai na SAFE, yana da muhimmanci ga tsaron yanki da ma na duniya, kamar yadda ministan tsaron Turkiyya Yasar Guler ya bayyana.
Guler ya jaddada a wata sanarwar da aka fitar ranar Alhamis cewa Turkiyya na cikin ƙasashe biyar da ke kan gaba wajen ba da gudunmawa ta dakaru ga ayyukan ƙawancen NATO da kuma matsayarta ta tsaro bayan taron ministocin tsaron ƙawancen NATO da kuma ƙawancen ƙasashe da ke taimaka wajen tsaron Ukraine a Brussels.
Ministan tsaron Turkiyya ya kuma jaddada jajircewar Ankara wajen sabunta rundunar tsaronta da ingantattun tsare-tsare da kuma kai ga manufar NATO na kashe kashi biyar cikin 100 na kasafin kuɗi kan tsaro.
“Mun jaddada gudunmawarmu ga Ukraine a matakin tattaunawar ɓangarori biyu da ta NATO, da kuma goyon bayanmu ga amfani da matakan diflomasiyya wajen samun tsagaita wuta da zaman lafiya,” in ji sanarwar.
Shiri domin ba da gudunmawa wajen samar da rundunar haɗaka ta Gaza
Ministan tsaro Guler ya kuma bayyana amincewa da tsagaita wuta da ake da shi yanzu a Gaza, yana mai kiransa a matsayin wata hanya ta mafitar samar da ƙasashe biyu masu adalci.
Ya yi kira da a yi cikakken aiwatar da tsagaita wutan tare da jaddada buƙatar agajin jinƙai babu ƙaƙƙautawa, yana mai alƙawarin cewa Turkiyya za ta ci gaba da ba da taimako.
Guler ya kuma ce rundunar sojojin Turkiyya a shirye take domin shiga dakarun haɗaka na ƙasa da ƙasa a Gaza, idan aka soma irin wannan aikin.
Isra’ila da Hamas sun aminc kan tsagaita wuta da shugaban Amurka Donald Trump ya jagoranta, domin kawo ƙarshen fiye da shekara biyu na kisan ƙare-dangin Isra’ila kan al’ummar Gaza, inda Tel Aviv ta kashe fiye da Falasɗinawa 60,000, yawancinsu mata da yara.
Turkiyya ɗaya ce daga cikin ƙasashen da suka ba da garanti kan yarjejeniyar da ƙasashe kamar Amurka da Masar da Qatar wajen tabbatar da tsagaita wuta.
A shekararta ta 70 da shiga ƙawancen NATO, Guler ya ce Turkiyya ta bayyana matsayarta kan batutuwa na tsaron yanki da na Turai ga ƙawayenta.
Turkiyya ta kuma rattaba hannu kan yarjejeniyar horaswa ta HVP wadda ke da manufar biyan buƙatar horaswa ta ƙasa da ƙasa a hanya mafi sauƙi.