Shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya ce ana ci gaba da aikata kisan kiyashi, kashe-kashe, hana fararen hula abinci da sauran munanan laifuka a Gaza a kullum, yayin da duniya ke kallon abin da ke faruwa. Ya zargi Isra'ila da mayar da yankin Falasdinawa na Gaza zuwa "gidan yari mafi girma a duniya."
"Kashe-kashen kiyashi, kisan gilla, nuna wariya, killacewa, hana abinci da sauran abubuwa da dama na ci gaba da faruwa kusan a kowace rana a gaban idanun duniya baki daya a Gaza, wanda gwamnatin Isra'ila ta mayar da shi gidan yari mafi girma a duniya," in ji Erdogan.
Shugaban na Turkiyya ya bayyana hakan ne a yayin wani taron kungiyar 'yan majalisar jam'iyyarsa mai mulki ta Adalci da Ci Gaba (AK Party), a Ankara, ranar Laraba.
Erdogan ya yi gargadin cewa ana fuskantar babbar matsalar jinkai a Gaza yayin da lokacin hunturu ke karatowa, inda ya dora alhakin hakan kan matakan takaita kayan agaji da Isra'ila ke aiwatarwa, wadanda ya bayyana a matsayin rashin tausayi.
Ya kuma nuna damuwarsa kan irin wahalhalun da yaran Falasdinawa ke fuskanta, yana mai bayyana yadda iyalai ke fama da ambaliyar ruwa kuma ba tare da samun isasshen matsuguni da zai kare su daga tsananin sanyi ba.
Haka kuma, Erdogan ya soki kasashen da suka dade suna bayyana kansu a matsayin masu kare dimokuradiyya da 'yancin dan Adam, yana mai cewa a yanzu an fara tona asirin munafuncinsu.
Da yake kira ga kasashen Musulmi da su kara daukar matakai kan halin da ake ciki, Erdogan ya ce ya kamata kasashen Musulmi su yi nazari mai zurfi kan irin matakin da suka dauka game da halin da ake ciki a Gaza.
"Maimakon mu dogara kacokan ga wasu, ya kamata mu a matsayinmu na Musulmi mu dauki mataki, tare da tabbatar da cewa an kara matsin lamba kan Isra'ila," in ji shi.
Ya bukaci kasashen Musulmi da su kara kaimi wajen kokarin kai agajin jinkai zuwa Gaza kafin yanayin hunturu ya kara tsananta.
"Mun shirya aika kwantenoni zuwa ga 'yan'uwanmu maza da mata da ke Gaza. Haka kuma, muna daukar matakan da suka dace dangane da kai agajin jinkai," in ji shi.
Erdogan ya kara da cewa, "Ko da wasu sun zuba ido sun yi kunnen uwar shegu, ba za mu yi shiru ba a kan zaluncin da ake yi a Gaza."
Ya jaddada cewa Turkiyya za ta ci gaba da sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na kai agajin jin kai, ko da kuwa ita kadai za ta kasance tana yin hakan.
Girmamar rashin zaman lafiya a duniya
Da yake magana kan manyan sauye-sauyen da ke faruwa a duniya, Erdogan ya yi gargadin cewa duniya na cikin wani yanayi na rashin tabbas sosai, yayin da fafatawar neman rinjaye tsakanin manyan kasashe ke kara tsananta.
"Muna cikin wani mawuyacin hali inda tsohon tsarin duniya ke durkushewa, babu wanda ya san tsarin da zai maye gurbinsa, sannan ana gudanar da fafatawa mai tsanani da barna fiye da yadda ake nunawa a kafafen watsa labarai da talabijin, a bayan fage," in ji shi.
Erdogan ya yi nuni da yakin da ke ci gaba tsakanin Rasha da Ukraine, da kuma karuwar tashe-tashen hankula a yankin Tekun Fasha, a matsayin misalan yadda rashin zaman lafiya ke kara kamari a duniya.















