Gwamnan jihar Filato da ke arewa maso tsakiyar Nijeriya, Caleb Muftwang, ya ce gwamnatinsa ta fara gurfanar da masu kai hare-hare a wani ɓangare na ƙoƙarin daƙile matsalar tsaron da jihar ta daɗe tana fama da ita.
Da yake magana ranar Jumma’a bayan ya gana da Shugaba Bola Tinubu a Legas, Mutfwang ya ce jihar tana samun ci-gaba wajen dawo da zaman lafiya da kuma sake samar da yarda tsakanin al’ummomi.
“Muna tunkararta ne ta hanyoyi biyu, hanya ta ƙarfi da ta laluma,” in ji gwanan.
“Muna ci gaba da tuntuɓar mutanenmu bisa buƙatar da ke akwai ta zaman lafiya da kuma buƙatar da ke akwai ta ci-gaba da girmama juna da girmama bil Adama,” in ji shi.
“Muna buƙatar sake gano yadda ake mutunta bil Adama ta yadda ba za mu buƙaci zubar da jini ba. Amma a lokaci ɗaya kuma, muna ƙoƙarin tabbatar da cewa an tabbatar da adalci. Mun fara gurfanar da mutane [a gaban kotu],” in ji gwamnan.
Gwamnan ya bayyana fatan cewa matakan da ake aiwatarwa za su samar da zaman lafiya mai ɗorewa.
“Akwai haske a ƙarshen rami. Abin da muke buƙata shi ne jajircewa. An samar da abubuwa da yawa; muna tsammani sosai cewa za su samar da sakamakon da ake so. Amma muna buƙatar jajircewa da kuma tabbatar da cewa ba mu ɗauke kafafunmu daga birki ba,” a cewarsa.
Mutfwang ya kuma bayyana cewa an ci gaba da tattaunawa tsakanin masu ruwa da tsaki bayan wata ganawa da Tinubu a baya game da yanayin tsaro a jihar Filato.
Ya ce an kafa wani ƙaramin kwamiti domin nazari kan batutuwan da ke ba da gudumowa ga rikicin da kuma ba da shawarwari game da mafita daga matsalar.
“Mun yi ƙoƙarin tabbatar da cewa shuwagabanni sun tabbatar da haɗin kai ta yadda mutane za su ga cewa kawunan shugabanninsu ba su rabu ba. Idan shuwagabannin suka yi aiki saɓanin wannan buƙatar, yana jinkirta tsarin kawo zaman lafiya zuwa jihar. Amma a yanzu muna samun ci-gaba ,” in ji shi.
Gwamnan ya ce sake gina yarda tsakanin al’ummomi da kuma dawo da ƙwarin gwiwa yana da muhimmanci ga tsarin samar da zaman lafiyar.






















