Tsohon shugaban Faransa Nicolas Sarkozy ya soma zaman gidan kaso ranar Talata bayan an same shi da laifin haɗa baki domin kashe kuɗaɗen da ya karɓa daga Libya domin yin yaƙin neman zaɓensa na shekarar 2007.
Sarkozy shi ne tsohon shugaban ƙasa na farko a tarihin Faransa a wannan zamani da zai yi zaman kurkuku, ko da yake ya musanta zargin da aka yi masa kuma wannan hukuncin na ba-sa-ban-ba ya ɗaure wa mutane kai.
Tafiyarsa daga fadar gwamnati ta Elysee Palace zuwa gidan kaso na La Sante mai ƙaurin suna a Paris ta ja hankalin ɗaukacin al’ummar Faransa.
Ɗaya daga cikin yaran Sarkozy, Louis, ya yi kira da a yi wani jerin gwano ranar Talata domin nuna goyon baya ga mahaifinsa a wata unguwa mai alfarma ta birnin Paris inda Sarkozy ke zama da matarsa, Carla Bruni-Sarkozy.
Shahararriyar mai tallan kayan ƙawar wadda ta zama mawaƙiya ta wallafa hotunan ‘ya’yan Sarkozy da waƙoƙi kansu a shafukanta na sada zumunta tun bayan da aka same shi da laifi.
Shugaba Emmanuel Macron mai matsakaicin ra’ayi da ke fuskantar ƙalubale ya karɓi baƙuncin Sarkozy a fadar shugaban ƙasa a makon da jiya.
“A ko da yaushe ina bayyanawa ƙarara cewa akwai ‘yancin kai na ɓangaren shari’a, amma a mataki na ɗan’adam daidai ne a karɓi baƙuncin ɗaya daga cikin waɗanda suka gabace ni a wannan yanayin,” a cewar Macron ranar Litinin.
Sarkozy ya shaida wa jaridar Le Figaro cewa yana tsammanin cewa za a riƙe shi inda ba zai ga kowa ba, sannan za a keɓe shi daga ko wane fursuna domin dalilai na tsaro.
Wani abu mai yiyuwa kuma shi ne a riƙe shi a ɓangren gidan kaso na “masu rauni”, wanda ake ce wa wuri na masu alfarma.
“Ba na tsoron kaso. Zan kasance cike da alfahari, ciki har da a gaban ƙofofin La Sante,” kamar yadda Sarkozy ya shaida wa jaridar La Tribune Dimanche . “Zan yi faɗa har zuwa ƙarshe.”
La Tribune Dimanche ta ruwaito cewa Sarkozy ya shirya jakar gidan kasonsa da tufafi da kuma hotuna 10 na iyalinsa da aka ba shi damar shiga da su.
Sarkozy ya kuma shaida wa jaridar Le Figaro cewa zai je da littatafai uku — iya adadin da aka ba da damar [shiga da su] — ciki har da littafin Alexandre Dumas’ “The Count of Monte Cristo”, wanda jaruminsa ya tsira daga wani gidan kaso da ke wani tsibiri kafin ya nemi ɗaukar fansa.
Alƙalin Paris ya yanke hukuncin cewa Sarkozy zai fara zaman kaso ba tare da jiran a ji ɗaukaka ƙararsa ba.
Bisa hukuncin, Sarkozy mai shekara 70, zai iya neman a sake shi ne kawai ga kotun ɗaukaka ƙara bayan ya soma zaman kaso, kuma alƙalai kana za su samu watanni biyu na aiki a kan buƙatar.