Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya naɗa tsohon babban hafsan tsaron ƙasar Janar Christopher Gwabin Musa a matsayin sabon Ministan Tsaron ƙasar.
Tinubu ya bayyana haka ne a wata sanarwa da kakakinsa, Bayo Onanuga ya fitar ranar Talata.
Sanarwar ta kara da cewa Shugaba Tinubu ya aika wasiƙa ga shugaban majalisar dattawan Nijeriya Godswill Akpabio inda ya sanar da shi naɗin da ya yi wa Janar Musa domin maye gurbin Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, wanda ya sauka daga muƙaminsa ranar Litinin.
Musa wanda zai cika shekara 58 a ranar 25 ga Disamba, ya yi aiki a matsayin Babban Hafsan Tsaro daga 2023 har zuwa Oktoban 2025 lokacin da Shugaban Kasa ya sauke shi daga mukaminsa a watan Oktoba, bayan wani yunkurin juyin mulki da aka yi na hana Shugaban Kasa.
Tsohon Babban Hafsan Tsaron, wanda aka gani a Fadar Shugaban Kasa a ranar Litinin, 1 ga Disamban ya yi wata ganawa ta sirri da Shugaban Kasa a ofishinsa da ke Fadar Shugaban Kasa, 'yan awanni kafin sanarwar murabus din tsohon Ministan Tsaro, Mohammed Badaru.
An haifi Janar Musa a Sokoto a shekarar 1967, kuma ya yi karatunsa na firamare da sakandare a can kafin ya halarci Kwalejin Nazarin Ci gaba da ke Zariya.
Ya kammala karatunsa a shekarar 1986 kuma ya yi rajista a Kwalejin Tsaron Nijeriya a wannan shekarar, inda ya sami digirin farko na Kimiyya bayan kammala karatunsa a shekarar 1991.
An tura Musa aikin Sojan Najeriya a matsayin Laftanar na Biyu a shekarar 1991 kuma tun daga lokacin yana gudanar da kyakkyawan aiki.












