| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Majalisar Wakilan Nijeriya ta nemi gwamnati ta bayar da rangwamen haraji ga kamfanonin jiragen sama
Wannan buƙatar ta biyo bayan tattaunawa kan karuwar farashin tikitin jirgi musamman a wannan lokaci na bukukuwan Kirisimeti.
Majalisar Wakilan Nijeriya ta nemi gwamnati ta bayar da rangwamen haraji ga kamfanonin jiragen sama
'Yan majalisar sun yi ƙorafi kan ƙaruwar kuɗin jirgin sama a ƙasar / Nigeria House of Representatives
17 awanni baya

A ranar Alhamis, Majalisar Wakilai ta nemi Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta bayar da rangwamen haraji nan take ga kamfanonin jiragen sama domin rage farashin tikitin jirgi a lokacin bukukuwan Kirsimeti.

‘Yan majalisa sun kuma nemi ragin kashi 50 cikin dari a wasu kudaden tallafi da ake cajin kamfanonin jiragen sama.

Wannan buƙatar ta biyo bayan tattaunawa kan karuwar farashin tikitin jirgi. Duk da haka, ‘yan majalisar sun ki amincewa da shawarar bayar da tallafi ga tikitin jiragen sama.

A ranar Talata, Majalisar Dattawa ta kira Ministan Sufurin Jiragen Sama na Nijeriya, Festus Keyamo, da sauran masu ruwa da tsaki kan karuwar farashin tikitin jirgi.

Sanata Buhari Abdulfatai daga Jihar Oyo, wanda ya jagoranci tattaunawar, ya shaida wa ‘yan majalisar cewa ‘yan Nijeriya na korafin karuwar farashin tikitin jiragen da ke zirga-zirga a cikin gida a cikin ‘yan watannin da suka gabata.

Abdulfatai ya bayyana cewa tikiti daya daga Abuja zuwa Legas yanzu yana kashe tsakanin N400,000 zuwa N600,000, wani adadi da yawancin ‘yan kasa ba za su iya biya ba.

“Dole ne mu gayyaci masu ruwa da tsaki a kamfanonin jiragen sama don su tattauna da binciko matsalolin. Dole ne a ɗauki matakai na gaggawa kafin lokacin bukukuwa,” in ji shi a lokacin zaman na majalisar.

Sauran ‘yan majalisa, ciki har da Sanata Adamu Aliero, sun bayyana ra’ayi iri daya.

Aliero ya ce ƙara farashin ba abin da za a amince da shi ba ne, yayin da Sanata Onyekachi Nwebonyi ya yi Allah wadai da abin da ya kira ƙaruwar kashi 400 cikin dari da ba a taba gani ba