Wata kotun sojin a Nijeriya ta musamman da ke zamanta a birnin Maiduguri na jihar Borno a Nijeriya ta yanke hukuncin ɗaurin-rai-da-rai ga wasu sojoji uku da kuma wani soji ɗaya da zaman gidan yari na tsawon shekaru 15 bisa samun su da laifin sayar da makamai ba bisa ka'ida ba ga ƙungiyoyin 'yan ta'adda.
An yanke wa sojojin hukuncin laifuka da dama, wadanda suka hada da sata, da yin mu’amala da harsasai ba bisa ƙa’ida ba, da kuma taimaka wa ‘yan ta’adda wadanda duk hukuncinsu ke karkashin dokar kotun.
Birgediya Janar Ugochukwu Unachukwu, mukaddashin kwamandan runduna ta 7 kuma kwamandan sashi 1, na Operation Hadin Kai (OPHK) ne ya jagoranci shari’ar ta kama mutanen da suka hadar da Raphael Ameh da Sergent Ejiga Musa da kuma Lance Corporal Patric Ocheje da laifin cinikayyar makamai da alburusai tsakaninsu da mayaƙan Boko Haram.
Kazalika kotun ta sami Omitoye Rufus mai rike da muƙamin Corporal da laifin haɗa baki wajen aikata wannan laifi, inda shi kuma aka yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru 15 a gidan yari.
The court ruled that their actions posed a direct threat to military operations and national security, constituting a clear case of aiding the enemy.
Kotun ta ce laifukan da suka aikata na barazana kai tsaye ga ayyukan soji da kuma tsaron ƙasa, wanda kuma a bayyane yake cewa hakan na taimaka wa maƙiya.