NIJERIYA
4 minti karatu
Jonathan zai iya takarar shugaban ƙasa a 2027, amma... —Fadar Shugaban ƙasar Nijeriya
Sanarwar ta ce Jonathan na da ‘yancin shiga takarar shugaban ƙasar idan yana so, kuma shuga Tinubu zai yi maraba da shi a fagen zaɓen idan ya yanke shwarar shiga takarar.
Jonathan zai iya takarar shugaban ƙasa a 2027, amma... —Fadar Shugaban ƙasar Nijeriya
Tsohon Shugaban Nijeriya, Goodluck Jonathan
10 awanni baya

Tsohon shugaban Nijeriya, Goodluck Jonathan, yana da ‘yancin takarar shugabancin ƙasar a zaɓen 2027 inda Shugaba Tinubu zai yi maraba da shi a fage fafatwa.

Wata sanarwar da mai bai wa Shugaba Tinubu shawara na musamman kan dabaru da watsa labarai, Bayo Onanuga, ya wallafa a shafinsa na X ta ce sai dai kotu ce za ta iya yanke hukuncin ko tsohonn shugaba Jonathan zai iya sake takara bayan ya sha rantsuwa sau biyu.

Sanarwar ta biyo bayan kalaman toshon ministan watsa labaran Nijeriya Farfesa Jerry Gana wanda ya ce Goodluck Jonathan zai yi takarar shugaban Nijeriya a shekarar 2027 a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar PDP domin dawo da kan mulki bayan shekara 12.

“Sai dai kuma, ya kamata mu yi wa tsohon shugaban ƙasa Jonathan hanunka mai sanda ya yi hankali ‘yan jam’iyyar PDP masu zaƙin baki da ke zuga shi. ‘Yan siyasa irin su Jerry Gana suna son su ja hankalinsa ya shiga takarar ne domin cim ma manufofinsu na siyasa da addini da ƙabilanci ne, “ in ji sanarwar.

“Za su yi watsi da shi a tsakiyar kogi, kamar yadda suka yi a shekarar 2015, kuma su ƙyale Jonathan da ba ya son hayaniya cikin matsala,” in ji Onanuga.

Sanarwar ta ce Jonathan na da ‘yancin shiga takarar shugaban ƙasar idan yana so, kuma shuga Tinubu zai yi maraba da shi a fagen zaɓen idan ya yanke shwarar shiga takarar. 

“Amma Jonathan zai shiga kotun ƙasa. Haƙiƙa kotu za ta tantance kan ko Jonathan, wanda aka rantsar a matsayin shugaban ƙasa sau biyu, ya cika sharuɗɗan kundin tsarin mulki kuma ya cancanci tayawa takarar shugaban kuma, idan ya yi nasara, a rantsar da shi a karo na uku,” a cewar Bayo Onanuga.

Ya ce duk da son kan manyan ‘yan siyasan PDP masu neman ya yi takara, Shugaba zai fuskanci hukuncin mutane game da ko yana da wani sabon abin da zai iya ba su bayan shekaru shidansa mai cike da masifa, lamarin da ya sa suka cire shi a zaɓen 2015.

Zargin albuzzaranci

Haka kuma Onanuga ya yi zargin cewa gwamnatin Jonathan ta yi almubazzaranci da kuɗin ƙasa kuma ya bar ƙasar cikin mawuyacin hali, inda, a cewarsa matsalar tattalin arziƙin Nijeriya ta samo asali.

“Jonathan da mai ba shi shawara kan tsaro, Kanar Sambo Dasuki (murabus) sun rarraba kuɗaɗen tsaro ga abokanai da yaransu. A shekarar 2010, Shugaba ya gaji daba biliyan $66, inda dala biliyan $46 ke cikin asusun ajiyan kuɗaɗen ƙ€tare kuma dala biliyan 20 cikin asusu rarar ɗanyen mai,” in ji shi.

Ya ce zuwa shekarar 2015 da ya bar mulki kuɗin da ke cikin asusun ƙetare ya koma dala biliyan 30 kuma kuɗin da ke cikin asusun rarar ɗanyen mai biliyan $2, duk da kuɗi mai tarin yawa da ya samu daga ɗanyen mai.

“A tabbace yake cewa tsakanin shekarar 2010 zuwa 2013, an sayar da gangar ɗanyen mai kan dala 100. Zuwa watan Disambar shekarar 2014, kuma gwamnatin Jonathan ta kasa biyan albashin ma’aikata,” in ji shi .

 “Ana  bin aƙalla jihohi 28 a faɗin ƙasar kuɗaɗen ma’aikata masu yawa, a cewarsa.

Ya ce aaɓanin haka kuma, shugaba Tinubu ya ɗauki matakai masu ƙarfi cikin watanni 28 da suka gabata domin yi wa tattalin arziƙin ƙasar garambawul.

Ya ƙara da cewa Shugaban Tinubu ya daidaita tattalin arziƙin cikin shekaru biyu da ya yi a kan mulki.

“A a tsakiyar shekarar 2025, tattalin arziƙin Nijeriya ya haɓaka da kashi 4.23 cikin 100 a ma’aunin GDP, ƙari mafi girma cikin shekaru hudu, lamarin day ya zarce hasashen asusun ba da lamuni na IMF,” in ji Onanuga.

 Ya kuma ce hawhwan farashi ya ragu zuwa kashi 20.12 cikin 100 a watan Agustan shekarar 2025, mataki mafi ƙaranci cikin shekaru uku.