KIMIYYA DA FASAHA
2 minti karatu
An fara baje-kolin fasahar jiragen sama ta TEKNOFEST a Istanbul
Taron TEKNOFEST, daya daga manyan baje-kolin kayan sufurin sararin samaniya da fasaha na janyo hankalin ɗaruruwan maziyarta.
An fara baje-kolin fasahar jiragen sama ta TEKNOFEST a Istanbul
Baje-kolin na gabatar da kayayyakin tsaro musamman na sama ga mahalarta: / AA
17 Satumba 2025

A ranar Larabar nan ne aka bude taron fasahar ƙere-ƙeren kayan sufirin sararin samaniya na Turkiyya TEKNOFEST a birnin Istanbul na kasar Turkiyya.

Gidauniyar Fasaha ta Turkiyya (T3) da Ma'aikatar Masana'antu da Fasaha ta Turkiyya ne suka shirya taron na kwanaki biyar, wanda ke gudana filin jirgin saman Ataturk da ke Istanbul.

Tun shekarar 2018 ake gudanar da TEKNOFEST tare da goyan bayan hukumomin gwamnati da dama, abokan aiki daga kamfanoni masu zaman kansu, da jami'o'i.

TEKNOFEST yana alfahari da adadin sabbin nau'ikan gasar da ake sabunta wa kowace shekara, TEKNOFEST ya ƙunshi manyan bangarori 58 da ƙananan rukunai 137.

Mahalarta daga ko'ina cikin duniya suna iya bayyana ilimi da gogewarsu, suna samun ci gaba mai mahimmanci a fagen cigaban fasahar kere-kere.

Fasaha, shauki da tashi sama

TEKNOFEST zai ci gaba da marabtar maziyarta har zuwa ranar Lahadi, kuma ba kawai tare da gasar nuna fasaha ba, har ma tare da ɗimbin abubuwan ban mamaki.

Bikin na nuna tashi da jiragen sama da ke kayatarwa, baje-kolin kayayyaki da dama, kayan fasaha, kayan kasuwanci na fasaha, da ayyukan tukin jiragen sama da dalibai za su yi, inda ake tattara abubuwan fasaha da ban sha’awa a lokaci guda.

An saba gudanar da bikin a garuruwa daban-daban na Turkiyya dub bayan shekaru biyu, inda a Istanbul kuma duk bayan shekaru uku.

An kuma gudanar da bikin a kasashen waje guda biyu: Azerbaijan da Jamhuriyar Turkawan Arewacin Cyprus.

A watan da ya gabata an gudanar da Blue Homeland, wani bangare na TEKNOFEST a Istanbul.

Bikin da aka gudanar a shekarar da ta gabata a birnin Adana na kudancin Turkiyya, TEKNOFEST ya ja hankalin maziyarta kusan miliyan 1.1, wanda ya zuwa yanzu kusan miliyan 11 ne suka halarta.