Nijeriya ta taka rawar gani a wasan da ta buga da Lesotho da ci 2-1 inda Nijeriya din ta fara jiyo ƙanshin yiwuwar halartar Gasar ta Cin Kofin Duniya ta 2026, musamman idan ta sake samun nasara a wasan da za ta buga nan gaba.
Sai dai duk da nasarar da ta samu a wasan na ranar Juma’a, a yanzu Nijeriya ita ce ta uku a rukunin, inda take bin bayan Benin da take a mataki na farko da Afirka a Kadu da ke a mataki na biyu.
A ranar Talatar makon gobe ne Nijeriya za ta kara da kasar Benin a wasanta na karshe na neman cancantar shiga Gasar ta Cin Kofin Duniya da za a buga a Amurka da Mexico da Canada.
Nijeriya tana bukatar samun nasara a wasan na makon gobe, wanda zai iya ba ta damar shiga gaban Afirka ta Kudu, musamman idan kasar ba ta yi abin a zo a gani ba a wasan da za ta buga da Rwanda.
A halin yanzu, Nijeriya na mataki na uku a teburin Rukunin C, inda take da maki 14 daga wasanni tara. Benin tana da maki 17 yayin da Afirka ta Kudu ke da maki 15.
Sabon tsarin gasar Kofin Duniya ya ƙunshi ƙasashe 48, inda Afirka take da gurabe 9 na ƙasashen da za su samu tikiti kai-tsaye, da kuma ƙarin ƙasashe huɗu ga waɗanda suka fi maki cikin na biyu a rukunoni tara.
Fatan Afrika ta Kudu ta gaza
Ga Nijeriya, sakamakon wasannin da aka buga a Talatar nan ya nuna irin jan aikin da ke gaban Nijeriya kafin ta samu gurbi cikin waɗanda za su ƙare a mataki na biyu a rukuninsu.
Ko da Nijeriya ta ci wasa dayan da ya rage mata, maki 17 kawai za ta iya samu.
Wannan na nufin dole Nijeriya ta yi fatan Afirka ta Kudu za ta ɓarar da maki.