| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Sojojin Nijeriya sun kashe 'yanta'addan Lakurawa, sun kuɓutar da mutane 62 a Kebbi da Zamfara
An kai farmakin tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro da ‘yan bijilanti na yankin, wanda hakan ya nuna irin haɗin kai da ke tsakaninsu domin yaƙi da ‘yanta’adda da ‘yanbindiga, a cewar wata sanarwa da Laftanal Kanal Olaniyi Osoba.
Sojojin Nijeriya sun kashe 'yanta'addan Lakurawa, sun kuɓutar da mutane 62 a Kebbi da Zamfara
Nigerian Army Rescue Operations / TRT Afrika Hausa
22 Janairu 2026

Rundunar sojin Nijeriya ta dakarunta da ke aiki a arewa maso yammacin ƙasar sun kashe wasu 'yanta'adda a Jihar Kebbi sannan sun kuɓutar da mutum 62 da aka yi garkuwa da su a Jihar Zamfara.

“Dakarun Haɗin Gwiwa na Operation Fansan Yamma da ke aiki a Sashe na 2 sun yi nasarar kashe 'yanta'adda biyu a Jihar Kebbi tare da kuɓutar da mutane 62 da aka yi garkuwa da su a Dajin Munhaye na Jihar Zamfara, a cewar wata sanarwa da Laftanal Kanal Olaniyi Osoba, Muƙaddashin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Sojin Nijeriya a Runduna ta 8 ya fitar ranar Laraba.

Ya ce an kai farmakin tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro da ‘yan bijilanti na yankin, wanda hakan ya nuna irin haɗin kai da ke tsakaninsu domin yaƙi da ‘yanta’adda da ‘yanbindiga.

An yi amfani da bayanan sirri wajen kai hari kan 'yan kungiyar ta'addanci ta Lakurawa kusa da kan iyaka tsakanin karamar hukumar Augie (Jihar Kebbi) da karamar hukumar Binji (Jihar Sokoto).

Masu AlakaTRT Afrika - Sojoji sun gano wurin da ’yan Boko Haram suke ɓoye man fetur a ƙarƙashin kasa a Borno

Sanarwar ta kara da cewa a farmakin da aka kai a kauyen Kerani, an samu nasarar kawar da 'yan ta'adda 2 tare da kwato babura 2 da 'yan ta'addar ke amfani da su. 'Yan ta'addar 2 suna sanye da kayan sarki kuma a kan babura 2.

A jihar Zamfara, sojoji a wani samame daban, sun kai farmaki a dajin Munhaye, wani wuri da shugaban 'yan ta'addar daji Kachalla Alti ke zama, bayan wani rahoton sirri da ya nuna cewa shugaban 'yan ta'addar ya yi garkuwa da wasu mutane.

Farmakin ya kai ga nasarar ceto mutane 62 da aka yi garkuwa da su wadanda yanzu haka suna tare da jami’an tsaro.

Sanarwar ta kuma ce ana ci gaba da kokarin sake hada wadanda aka kubutar da iyalansu.

Waɗannan ayyukan sun nuna kokarin da jami’ai ke yi wajen kaddamar da Farmakan Fansar Yamma tare da abokan aikinsu don kawar da ‘yan ta’adda a yankin, in ji sanarwar.