Sojojin ruwan Amurka takwas sun jikkata bayan harin makami mai linzami na Iran kan wani jirgin ruwa a Mashigar Hormuz, a cewar rahoton kafar NBC News, tana mai ambato jami'an Amurka uku.
Sojojin ruwan ba su samu mummunan rauni ba amma sun shaƙi hayaƙi da kuma buguwa a kai, yanayin da ya jawo tsananin ciwon kai wanda ake ganin ya taɓa lafiyar ƙwaƙwalwarsu, in ji rahoton.
Rundunar ta ƙunshi ƙananan jami’ai bakwai da kuma wani babba guda ɗaya, dukkansu suna aiki a matsayin wani ɓangare na bataliyar sojoji lokacin da harin ya auku a ranar 14 ga Satumba.
Dukka sojojin takwas sun koma bakin aiki jim kaɗan bayan harin, kamar yadda jami'ai suka tabbatar.
Jami'an sun bayyana cewa jirgin ruwan da aka kaiwa hari ba jirgin ruwan yaƙin Amurka ba ne da aka tura, sai dai ba su bayyana asalinsa ba.
Rahoton mutuwar jami'an tsaron Amurka
Lamarin ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da bincike kan adadin asarar rayuka ta jami’an Ma'aikatar Tsaro tun bayan ɓarkewar yaƙin Amurka da Isra'ila da Iran a watan Fabrairu, inda jimillar adadin waɗanda suka jikkata da waɗanda suka mutu ke ci gaba da sauyawa a rahotanni da ake tattarawa.
Ya zuwa ranar Laraba, Tsarin Nazarin Mutuwar Jami'an Tsaron Amurka (DCAS) ya tattaro sunayen sojojin Amurka 861 da suka jikkata sakamakon yaƙin.
An sanya sunan dakarun sojin Amurka takwas a cikin rajistar bayanan waɗanda suka mutu bayan kwanaki 10 da harin na ranar 14 ga Satumba.
Wani jami'in tsaron Amurka ya danganta jinkirin da aka samu wajen tantance alƙaluman waɗanda suka mutu ko suka jikkata saboda wasu alamomin rauni ba sa bayyana sai bayan wasu kwanaki da kuma rashin iya samun rahoto a ainihin lokaci daga tsarin bin diddigin waɗanda suka mutu ko suka jikkata.






















