| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Victor Osimhen, Zaidu Sanusi da Muhammad Usman na cikin ‘yan Super Eagles da za su je AFCON 2025
Fitaccen ɗanwasan Super Eagles, Victor Osimhen, da ke murza leda a Galatasaray ta Turkiyya da Ademola Lookman da Akor Adams da Moses Simon na cikin jerin ‘yanwasan da za su fafata a gasar AFCON 2025 a ƙasar Maroko.
Victor Osimhen, Zaidu Sanusi da Muhammad Usman na cikin ‘yan Super Eagles da za su je AFCON 2025
Super Eagles ta kai wasan ƙarshe na gasar a shekarar 2023 / Reuters
12 Disamba 2025

Kocin Super Eagles,  Eric Chelle, ya fitar da jerin sunayen ‘yan wasa 28 da za su wakilci tawagar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya a gasar cin kofin Afirka ta AFCON 2025 da za a fara a ƙasar Maroko a watan Disamba.

A cikin jerin ‘yan wasan da kocin ya fitar ranar Alhamis, akwai Zaidu Sanusi wanda yake buga wasa a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Porto da ke ƙasar Portugal.

Kazalika akwai Usman Muhammad Edu, ɗan wasan tsakiya da ke taka leda a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Ironi Tiberias ta Isra’ila.

Akwai kuma Salim Fago Lawal, wani ɗanwasan gaba da ke taka leda a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta NK Instra 1961 ta ƙasar Croatia.

Fitaccen ɗanwasan Super Eagles, Victor Osimhen, da ke murza leda a Galatasaray da Ademola Lookman, mai wasa a Atalanta na Italiya da Akor Adams na Sevilla da Moses Simon na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Paris na cikin jerin ‘yanwasan da za su wakilci Nijeriya a gasar.

Har wa yau akwai Kelvin Bassey da ke taka leda a Fulham da Semi Ajayi na Hull City da Bright Osayi-Samuel da ke wasa a Birmingham City da Bruno Onyemaechi da ke taka leda a Girka.

Kazalika a cikin jerin ‘yanwasan akwai Wilfred Ndidi da ke wasa a Besiktas da Frank Onyeka da ke Brentford da Fisayo Dele-Bashiru da ke wasa a Lazio da Alex Iwobi da ke wasa a Fulham.

Akwai kuma Stanley Nwabali wanda ke kama gola a Chippa United ta Afirka Ta Kudu da Francis Ozoho da ke kama gola a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Omonia da ke Cyprus.

Ranar 21 ga watan Disamba ne dai za a fara gasar cin kofin Afirka ta AFCON 2025 inda ƙasashe 24 za su fafata domin neman cin kofin Afirka.

Rumbun Labarai
Rundunar Sojin Nijeriya ta ce ta daƙile hare-haren 'yan ta'adda a jihar Borno
Nijeriya ta gargaɗi ‘yan ƙasar kan faɗawa tarkon masu ɗaukar ma’aikata su tura su wurin yaƙi
'Yanbindiga sun kashe aƙalla mutum 30 a Jihar Neja ta Nijeriya, sun ƙona ofishin 'yansanda
'Yanbindiga sun kashe DPO na 'yansandan Nijeriya a Jihar Katsina
'Rashin sake wa hukumomin gwamnatin Nijeriya kuɗaɗen kasafi koma-baya ne ga ci gaban ƙasa'
Za a yi zaben Shugaban Kasa a Nijeriya ranar 20 ga Fabrairun 2027, in ji INEC
Hukumar Kiyaye Haɗɗura ta Nijeriya ta kori ma'aikatanta 43 kan saɓa wa dokar aiki
Jami'an tsaro sun ƙwace fasfon Nasir El-Rufa'i bayan yunkurin kama shi ya ci tura a filin jirgi
Sojojin Nijeriya sun kashe 'yan Boko Haram 16 a Borno
CBN ya bai wa 'yan canji a Nijeriya damar sayen dala 150,000 a duk mako daga gwamnati
Amurka za ta tura sojojinta 200 Nijeriya
Sojojin Nijeriya sun kashe gomman 'yan-ta'adda, sun dawo da mutum 700 gida a arewa maso gabas
Me ya sa Kannywood ke fafutuka yayin da Nollywood ke samun tagomashi?
Shugaban Hukumar Alhazan Nijeriya Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan ya ajiye aikinsa
Mutum fiye da 30 sun rasu sakamakon hatsarin mota a Jihar Kano
Nijeriya: 'Yanbindiga sun sace wani faston Katolika a Kaduna, sun kashe mutum uku
Nijeriya da Nijar sun ƙulla yarjejeniya kan jigilar kayayyaki da tsaron kan iyaka
Shugaba Tinubu na Nijeriya na shirin kai ziyarar aiki London a watan Maris
Jerin hare-hare sun yi sanadin mutuwar mutum 30 a Jihar Benue ta Nijeriya
Jami’an tsaron Nijeriya sun kwance wani bam da ‘yan ta’adda suka dasa a Zamfara