Aure, siyasa da shugabanci: Darussan da ke tattare da dambarwar auren Gwamnan Kano
Zainab ’ya ce ga tsohon gwamnan Kano kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya riƙe ta tun tana ƙarama har zuwa aurenta. / TRT Afrika Hausa
Aure, siyasa da shugabanci: Darussan da ke tattare da dambarwar auren Gwamnan Kano
A wasu lokuta, rikicin aure kan wuce tsakanin ma’aurata biyu, ya shafi iyali, zumunta, siyasa da ma al’umma. Wannan ne ya sa dambarwar auren Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da Zainab Rabiu Kwankwaso ta dauki hankalin jama’a.
 

Dambarwar auren Abba Kabir Yusuf da Zainab Rabiu Kwankwaso ta sake tayar da muhawara kan sirrin iyali, dangantakar siyasa da nauyin shugabanci. Amma ina iyakar da ya kamata a kiyaye tsakanin rayuwar mutum da mukaminsa na gwamnati?

A wasu lokuta, rikicin aure kan wuce tsakanin ma’aurata biyu, ya shafi iyali, zumunta, siyasa da ma al’umma. Wannan ne ya sa dambarwar auren Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da Zainab Rabiu Kwankwaso ta dauki hankalin jama’a.

Zainab ’ya ce ga tsohon gwamnan Kano kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya riƙe ta tun tana ƙarama har zuwa aurenta. Kwankwaso ya kuma taka muhimmiyar rawa wajen gina tafiyar siyasar Abba, inda ya mara masa baya a zaɓen gwamna na 2023.

Sai dai daga baya, dangantakar siyasa tsakanin Abba da Kwankwaso ta yi tsami, har suka rabu a tafiyar siyasa.

Rahotanni sun ce Zainab ta garzaya kotu a Abuja domin neman a raba aurensu. A ranar 16 ga Nuwamba, Abba ya yi wasu kalamai a wajen wani taro da ’yan fansho a gidan gwamnatin Kano, waɗanda suka ƙara jawo hankalin jama’a kan batun rabuwar auren.

A jawabin nasa, gwamnan ya ce kasancewarsa da mata ɗaya ya rage masa matsayi daga “Corporal” zuwa “Constable”. Ya kuma yi maganar yiwuwar ƙara aure a nan gaba, har da barkwanci kan sanya tallan neman sabuwar mata.

Wannan lamari ya sake tayar da muhawara kan wasu tambayoyi: Ina iyakar sirrin iyali take idan ɗaya daga cikin ma’auratan shugaba ne? Shin ya dace a mayar da irin wannan batu abin raha a taron jama’a? Kuma ta yaya za a kare mutuncin ma’aurata da ’ya’yansu idan rikicin aure ya fito fili?

Sirrin aure da haƙƙin ma’aurata

A ɓangaren Zainab, neman raba aure ta hanyar kotu haƙƙi ne da doka ta ba ta. Sai dai wasu na tambayar ko ya dace a nemi a gudanar da shari’ar cikin sirri, musamman ganin irin tasirin da batun zai iya yi ga iyali.

Duk da haka, babu wata hujja da ke nuna cewa Zainab ce ta fitar da bayanan shari’ar ga manema labarai.

A Nijeriya, galibi ana gudanar da shari’o’in kotu a bayyane, ko da yake kotu na iya ɗaukar matakan kare bayanan sirri idan akwai dalilai na musamman.

A nasa ɓangaren, Abba ma yana da ’yancin bayyana matsayinsa kan rayuwarsa. Sai dai kasancewarsa gwamna na nufin kalamansa ba sa tsaya wa a wajen da ya furta su; suna iya zama abin nazari da muhawara a tsakanin jama’a.

Wata tambayar da ta taso ita ce ko yin barkwanci kan neman sabuwar mata a wajen taron hukuma shi ne salon da ya fi dacewa da girman mukamin da yake riƙe da shi.

Lokacin da siyasa ta shiga cikin aure

Malam Kabiru Sufi, mai sharhi kan siyasa, ya ce idan dangantakar aure ta haɗu da siyasa, wajibi ne a yi taka-tsantsan domin kada a lalata alakar da ke tsakanin ɓangarorin.

A cewarsa, ya kamata kowane ɓangare ya yi ƙoƙarin dakile tasirin rikicin kafin ya shafi zumunta da dangantakar ɗan’adamtaka ta dogon lokaci.

Sufi ya yi nuni da cewa akwai aurarraki a Arewacin Nijeriya da suka haɗa iyalai masu ƙarfin siyasa a jam’iyyu mabambanta, inda ma’auratan ke ƙoƙarin ware bambance-bambancen siyasa daga zaman aurensu.

Ya yi gargaɗin cewa idan aka bar rikici ya yi nisa, magoya bayan ɓangarorin na iya shiga cikin abin da bai kamata ya zama fagen siyasa ba.

Wannan ya nuna yadda rikicin da ya fara a tsakanin ma’aurata zai iya shafar dangantakar iyalai da kuma faɗaɗa sabani a tsakanin masu goyon bayan siyasa.

Muhimmancin iya sarrafa motsin rai

Wani muhimmin batu da ya sake fitowa fili a wannan dambarwa shi ne iya sarrafa motsin rai, wato Emotional Intelligence.

Wannan na nufin fahimtar abin da mutum yake ji, sarrafa yadda zai mayar da martani, da kuma la’akari da yadda kalamansa ko ayyukansa za su shafi wasu.

Ba wai kawai danne damuwa ko ɓoye fushi ba ne. Ya haɗa da sanin lokacin da ya dace a yi magana, yadda za a yi ta, da kuma fahimtar sakamakon abin da mutum ya faɗa ko ya aikata.

Dr Hadi Musa, masanin zamantakewa, ya ce matsayin da gwamna yake kai ne ya ƙara ɗaukaka batun a idon jama’a, duk da cewa aure da matsalolin da ke tattare da shi al’amura ne na ɗan’adamtaka da kowa zai iya fuskanta, ko mai mukami ne ko talaka.

Sai dai ya ƙara da cewa idan mutum yana jagorantar al’umma, ana sa ran ya zama abin koyi wajen yadda yake tafiyar da rayuwarsa.

Dr Hadi ya kuma ce shugabanni da iyalansu na buƙatar samun ƙwararru da za su riƙa ba su shawara kan kula da motsin rai da yadda za su tafiyar da matsalolin rayuwarsu.

Ko da yake ya ce kuzarin shugabanni na iya ƙarewa wajen gudanar da al’amuran jama’a, hakan bai kamata ya hana su kula da rayuwar iyalansu ba.

Wace rawa al’umma za ta taka?

A irin wannan batu, al’umma ma na da rawar takawa. Bai kamata a mayar da rikicin aure abin nishaɗi ba, ko kuma kowa ya yi gaggawar sharhi kan abin da bai da cikakkiyar masaniya a kai.

Haka kuma, ya kamata a guji yaɗa bayanan sirrin yara ko danganta kowace matsalar iyali kai tsaye da siyasa ba tare da hujja ba.

Mutunta sirrin iyali da tausaya wa waɗanda abin ya shafa na daga cikin nauyin da ke kan al’umma, musamman a lokacin da rikici ya zama abin tattaunawa a bainar jama’a.

Darasin da rikicin ke koyarwa

Wannan lamari ya nuna yadda aure, zumunta, mulki da siyasa za su iya haɗuwa a rayuwar manyan mutane. Amma kuma ya tuna mana cewa shugabanni ma mutane ne, masu fuskantar matsalolin rayuwa irin na sauran al’umma.

Malam Kabiru Sufi ya ce ya kamata a samu dattawa da masu faɗa a ji, musamman malaman addini, da za su shiga tsakani domin rage zafin rikicin.

Ya kuma yi kira ga ɓangarorin biyu da su nuna juriya da haƙuri wajen dakile duk wani abu da zai ƙara rura wutar saɓani, musamman yayin da Nijeriya ke tunkarar zaɓen 2027.

A ƙarshe, mu ma masu sharhi muna da rawar da za mu taka: mu guji gaggawar yanke hukunci kan abin da ba mu da cikakken sani a kai. Kamar yadda masu magana kan ce, tsakanin mata da miji sai Allah.

Ba abin mamaki ba ne a nan gaba a ga Abba da Zainab sun ƙulla dangantaka mai kyau fiye da yadda take a baya. Saboda haka, ya dace a bar ƙofa a buɗe ga sulhu, maimakon ɗaukar cewa rikicin yau shi ne ƙarshen dangantakarsu.