Daga ƙasusuwa zuwa abin kwaɗayi: Orenge, abincin da ke sanya santi a Nairobi
RAYUWA
3 minti karatu
Daga ƙasusuwa zuwa abin kwaɗayi: Orenge, abincin da ke sanya santi a NairobiKai da ƙafar kaza ‘Orenge’ sun zama wani abinci mai daɗi da mutane daga kowane fanni na rayuwa ke jin daɗinsa a birnin Nairobi na ƙasar Kenya.
Ga araha, ga daɗi, 'Orenge'—ƙafafun kaza—ya zama ɗaya daga cikin abincin da ya yi fice akan titunan Nairobi / TRT Afrika
3 awanni baya

Ba dankali ba ne ko nama — wani abinci ne da idan mutum ya ci dole sai ya dawo.

Barka da zuwa titunan Nairobi, inda wani abinci da ke da araha ya zama abin da kowa ke so— ga kuma ɗanɗano: ƙafafun kaza.

Ana kiran shi da 'Orenge' a harshen al'ummar Luo da 'Virenje' a cikin Luhya, kuma ya wuce ya kira shi da abinci kawai—abin ci ne na al'ada.

"Aikina shi ne sayar da 'Orenge.' Mutane suna kirana da Mama Orenge," a cewar Fidelis Kavutha.

Wannan shi ne abincin kwaɗayi da ke jawo hankali a Nairobi.

"Na kwashe tsawon shekaru 30 ina sayar da 'Orenge'. Kowa yana cin su—marasa ƙarfi da masu kuɗi. Ni ma ina cin su kuma ina ganin suna da daɗi sosai. Shi ya sa nake sayar da su." kamar yadda Margaret Kariuki mai sayar da kaji ta shaida wa TRT Afrika.

"Waɗannan kai da ƙafafuwan na kaji su ne abin da kowa ke so a gidajenmu. Ana samunsu a ko da yaushe kuma suna da araha ga kowa," in ji Kevin Mutiso, wani da ke sayen kai da ƙafafuwa na kaza.

"Ina son su saboda suna da araha kuma suna da daɗi. Idan ka ci su… kawai suna da daɗi," a cewar wata mai saye Faith Muema.

"Waye ba zai iya sayen kai da ƙafa na kaza ba? in ji Muhat Kanyo yana mai ƙari da cewa, Faɗa mini—waye? duk lokacin da na ci su, ina ji kamar an sake haihuwata”

Ga mutane da yawa, ba wai kawai ɗanɗano ba ne— wani yanayi ne na daban. Gutsira ɗaya, kawai mutum zai ji yana son zama a Nairobi.

"Ina son ƙasusuwan. Suna kuma taimaka mana ta hanyar samar da sinadarin calcium. Kuma suna da araha," in ji wani Edwin Kinyua.

Ga masu sayarwa, 'Orenge' suna samun ciniki da riba mai gwaɓi.

"Kowace rana ina sayar da kilo huɗu na ƙafar kaza a shilling 100 na kuɗin Kenya. Kuma ina sayar da su duka a shilling 1,000. Bayan sayen su a kan shilling 400, ina samun ribar 600 - wani lokacin ma har 700 ko 800," kamar yadda Fidelis Kavutha da ke kasuwancin kai da ƙafa na kaza ta shaida wa TRT Afrika.

"Ba ka cin 'Orenge' don ka cika cikinka - kana cin sa ne don ɗanɗano, yanayi, da kuma karɓuwa da ya samu a wurin jama’a. Sannan akwai hikima a cikinsa. Ba a ci da cokali mai yatsu, kuma babu gaggawa. Da hannu kawai, sai ɗanɗano, da kuma yanayi mai kyau... sai godiya ga Allah!

Baya ga sayar da shi a kan tituna, masana abinci masu gina jiki sun ce akwai sinadarai masu yawa da ake samu a ƙafar kaza.

"Ƙafafun kaza suna da wadataccen sinadarin calcium, wanda yake da kyau ga lafiyar ƙashi, da haƙora. Haka kuma suna ɗauke da sanadarin collagen, wanda ke tallafa wa laushin fata. Bugu da ƙari, suna da glucosamine da chondroitin, waɗanda ke ƙarfafa gaboɓin jiki," a cewar masanin abinci mai gina jiki David Kauguima ga TRT Afrika.

Akan dafa shi a kan gawayi, bayan an zuba gishiri da kayan ƙanshi, sannan da zafinsa ake sayarwa —‘Orenge’ abincin kwaɗayi ne mai sauƙi, ga araha, kuma duk wanda ya ci sai ya dawo.

Abu ɗaya da ke da tabbaci shi ne: a Nairobi, ba za ku iya yin watsi da ƙasusuwan nan ba.