NIJERIYA
1 minti karatu
Hukumar DSS a Nijeriya ta kori ma'aikatanta fiye da 100
Hukumar ta bayyana hakan ne a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X a ranar Talata, tana mai cewa matakin ya biyo bayan sauye-sauyen da take ci gaba da aiwatarwa domin inganta ayyukanta.
Hukumar DSS a Nijeriya ta kori ma'aikatanta fiye da 100
Hukumar tsaro ta farin kaya a Nijeriya (DSS) ta kori ma'aikatanta 115
13 awanni baya

Hukumar tsaro ta farin kaya a Nijeriya (DSS) ta sanar da korar ma’aikatanta 115, tana mai gargaɗin jama'a game da hulɗa da duk wani mutum da ke bayyana kansa a matsayin jami'in hukumar.

Hukumar ta bayyana hakan ne a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X a ranar Talata, tana mai cewa matakin ya biyo bayan sauye-sauyen da take ci gaba da aiwatarwa domin inganta ayyukan ta.

“A wani ɓangare na sauye-sauye da hukumar DSS ke ci gaba da aiwatarwa, ana sanar da jama’a cewa an kori ma’aikata 115 daga aiki” in ji sanarwar.

Hukumar DSS ta wallafa hotuna da kuma sunayen ma'aikatan da korar ta shafa, tare da gargaɗin jama'a da su yi taka-tsantsan wajen yin hulɗa da wasu waɗanda ta bayyana sunayen su a matsayin Barry Donald da Victor Onyedikachi Godwin waɗanda har yanzu suke shiga tare da nuna kansu a matsayin jami’an DSS don zambatar ‘yan Nijeriya.

"Ana shawartar jama'a da su guji mu’amala da ta shafi hukumar da waɗannan mutanen da Hukumar ta kora," in ji sanarwar ta DSS.

Kazalika hukumar ta wallafa lambar waya da kuma adireshinta na intanet ga ‘yan Nijeriya da ke buƙatar ƙarin bayani dangane da korarrun ma'aikatan.