WASANNI
2 minti karatu
Amad Diallo: Ɗan wasan Man U zai je hutu saboda mutuwar mahaifinsa
Amad Diallo, Noussair Mazraoui, da Casemiro ba za su buga wasan wannan ƙarshen makon ba a cewar koci Ruben Amorim.
Amad Diallo: Ɗan wasan Man U zai je hutu saboda mutuwar mahaifinsa
Shekarun Amad Diallo 23 a duniya / Reuters
3 awanni baya

Ɗan wasan gaban Manchester United ɗan asalin Ivory Coast, Amad Diallo ba zai buga wasan da ƙungiyarsa za ta kara da Brentford ba a Gasar Firimiya na ƙarshen makon nan.

Kocin United Ruben Amorim ya yi jawabi a ranar Jumma’a kan rasa Diallo da wani ɗan wasan Noussair Mazraoui a cikin tawagar, inda rahotanni suka ce mahaifin Amad ne ya rasu.

Ya faɗa wa manema labarai gabanin wasansu na Asabar cewa, "Amad ba zai zo ba. Wani daga iyalansa ya rasu, don haka muna jajanta wa Amad".

Wasu rahotanni na cewa Diallo, wanda ya buga duka wasanni shida na United a kakar bana, ya goge duka hotunansa a Instagram bayan shan suka saboda rashin ƙwazonsa a wasansu da suka doke Chelsea da ci 2-1 ranar Asabar.

Amorim ya ƙara da cewa, "A kullum ina gaya wa ‘yan wasana, su kashe soshiyal midiya".

‘Za mu iya nasara’

"Yanayi ne matsananci gare shi kuma a wannan yanayi wasa na gaba ba shi da mahimmanci. Za mu iya lashe wasan nan ba tare da Amad ba kuma muna so mu yi nasara domin sa."

Amorim ya ce Mazraoui ma ba zai buga wasa ba bayan da jaridun Burtaniya suka ruwaito cewa ɗan wasan ɗan asalin Morocco bai je atisaye ba saboda rauni.

Shi ma ɗan wasan baya, Casemiro an dakatar da shi daga buga wasan na Asabar saboda sallamarsa da aka yi a wasansu da Chelsea.

Manchester United dai ta ci maki bakwai daga wasanni biyar, kuma tana fatan cin wasanni biyu a jere a karon farko a kakar bana a wasan nasu da Brentford.