Rundunar sojin saman Nijeriya (NAF) ta ce saukar jirginta ƙirar C-130 a Burkina Faso ya faru ne domin kauce wa hatsari kuma ta bi hanyar da ta dace.
Darakatan watsa labarai na hedikwatar rundunar sojin saman Nijeriya, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya ce jirgin ya sauƙa ne a ƙasar ta yammacin Afirka saboda “matsalar na’ura”.
“Rundunar sojin saman Nijeriya tana son ta yi bayani kan rahotanni game da yada zangon jiginta ƙirar C-130 a kan hanyarsa ta zuwa ƙasar Portugal ranar 8 ga watan Disamba na shekarar 2025.
Bayan tashin jirgin daga Legas, jami’ai sun lura da wata matsalar na’ura lamarin da ya tilasta saukarsa a Bobo-Dioulasso, Burkina Faso, filin jirgi mafi kusa, kamar yadda ya dace a tsarin kariya da na tuƙin jirgi a duniya,” a cewar Ejodame a wata snaarwar da ya fitar ranar Talata.
Rahotanni dai sun ce hukumomin Burkina Faso sun kama jami’ai 11 kan keta sararin samaniyarta.
Sai dai kuma, Ejodame ya ce dukkan jami’an rundunar sojin saman Nijeriyar “suna cikin aminci kuma sun samu tarba mai kyau daga hukumomin da suka karɓe su”.
“Ana shirin ci gaba da tafiyar kamar yadda aka tsara ,” in ji sanarwar.
Rundunar sojin saman Nijeriya ta miƙa godiyarta ga ‘yan Nijeriya bisa goyon bayan da ta samu “a wannan lokacin ” kuma ta tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa za ta ci gaba da martaba tsare-tsare na aiki da kariya.
AES ta yi Allah wadai
Ƙasashen yankin Sahel AES sun yi Allah wadai da saukar gaggawar da jirgin ɗaukar kaya na sojin Nijeriya ya yi a Burkina Faso ranar Litinin, inda suka yi barazanar ɗaukar mataki kan duk wani yunƙuri na keta alfarmar sararin samaniyarsu.
Ƙasashen AES - waɗanda suka haɗa da Mali da Nijar da kuma Burkina Faso - sun bayyana a wata sanarwa ta haɗin gwiwa cewa jirgin na ɗauke ne sojoji 11 kuma ba shi da izinin wucewa ta saman Burkina Faso.
"Wani jirgi na sojin saman Jamhuriyar Tarayyar Nijeriya, samfurin C-130, ya sauƙa ala tilas a yau a Bobo Dioulasso, Burkina Faso, bayan ya samu yanayin matsalar gaggawa a lokacin da yake tafiya a sararin samaniyar Burkina Faso," in ji wata sanarwar AES da aka karanta a kafafen watsa labaran gwamnati a na ƙasashen na yammacin Afirka.
Ƙeta sararin samaniya
Sanarwar ta bayyana sauƙar jirgin a matayin wani “mataki na gaba” kuma ta ce sojojin saman ƙasashen suna jiran ko ta kwana a sararin samaniyar ƙasashen kuma an ba su damar “yin kaca-kaca da kowane jirgi” da aka ga ya keta sararin samaniyar ƙasashen ƙungiyar.
Sanarwa ta haɗin gwiwa ba ta bayyana abin da ya faru da jami’an sojin saman Nijeriya 11 da suke cikin jirgin Nijeriyar ba.
Ƙasashen Sahel ɗin uku, da suke fama da ƙungiyoyin ‘yan ta’adda a yankin Sahel, suna zaman doya da manja ne da ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Yammacin Afirka ECOWAS mai maƙwabtaka.
A watan Janairu, ƙasashen suka fice daga ƙungiyar ECOWAS bayan sun kafa tasu ƙungiyar.
Ƙasashen uku sun kuma nesanta kansu daga Ƙasashen Yamma, musamman tsohuwar uwargijiyarsu Faransa yayin da suke matsawa kusa da Rasha.














