Masanin kimiyya na Turkiyya ya jagoranci 'yan sama jannati wajen gano sabbin duniyoyi
Masanin kimiyya na Turkiyya ya jagoranci 'yan sama jannati wajen gano sabbin duniyoyi
Masanin kimiyya na Turkiyya ya jagoranci 'yan sama jannati wajen gano sabbin duniyoyi
Tawagar ta gano duniyoyi da ke zagayen wasu taurari uku, ciki har da TOI-5799c, wacce akwai yiwuwar sararin samaniyarta da yanayinta su iya daukar ruwa.
11 Nuwamba 2025

Wata tawagar ‘yan sama jannati karkashin jagorancin masanin kimiyya na Turkiyya Selcuk Yalcinkaya, sun gano sabbin duniyoyi da ke wajen Duniyar Rana — akwai yiwuwar za a iya rayuwa a ɗaya daga cikinsu da take bangaren ciki na yankin da tauraruwarta take, wacce kuma ke da sararin samaniya.

Wadannan duniyoyin suna da nisa kusan shekarun haske 90 daga duniyarmu ta Earth.

An gano cewa — biyu daga duniyoyin suna zagaye karamar tauraruwar mai sanyi mai suna TOI-5799, sai kuma kowace daya na zagaye taurarin TOI-1743 da TOI-6223, kuma an yi binciken ne ta hanyar amfani da bayanai daga Hukumar Bincike ta AU Kreiken Observatory da Turkish National Observatory.

Wadannan binciken sun kasance wani ɓangare na aikin digirin-digirgir na Yalcinkaya mai taken 'ganowa da tabbatar da duniyoyi guda huɗu daga girman super-Earth zuwa Neptune a kusa da taurarin M-dwarfs', wanda aka buga a mujallar Astronomy & Astrophysics ta watan Oktoban 2025.

An gano daya daga cikin duniyoyin na wajen Duniyar Rana tana kewaya TOI-5799, wacce ake kira TOI-5799c, inda aka fahimci cewa tana cikin yankin da zai iya tallafa wa rayuwa na wannan tauraruwa, duk da kasancewarta mai nisan kimanin shekarun haske 90 daga Duniyar Earth.

Yalcinkaya ya shaida wa Anadolu cewa tawagarsa ta gano duniyoyin da ke wajen Unguwar Rana wato exoplanet ne bayan ganowar da abin gangen nesa na TESS Space Telescope ya yi.

Telescope ɗin na bibiyar siginar tafiya (transit) na tsawon kwanaki 30 a sararin samaniya, yayin da masana a Duniya ke amfani da manyan tauraron hangen nesa na observatory don gano wane tauraro ne a yankin ke fitar da siginar da kuma tantance ko siginar ta fito daga wannan tauraron ne ko wani kusa da shi.

Yiwuwar zama mazaunin rayuwa

"Daya daga cikin duniyoyin da muka gano, TOI-6223b, ta kai girman Neptune amma tana matukar kusa da tauraruwarta, shi ya sa ake kirana 'hot Neptune'," ya ce. "Yayin da radius ɗinta yana kama da na Neptune, muna buƙatar duba irin iskar da ke cikin yanayinsa."

"A gefe guda, ɗayar kuma, TOI-1743b, super-Earth ce — kimanin kashi 70 cikin ɗari ta fi duniyarmu girma kuma duniyar ƙasa ce (terrestrial)," ya lura. "Wataƙila ba za ta iya riƙe iskar mai yuwuwar bacewa a yanayinta ba — kuma tana matukar kusa da tauraruwarta don haka tana da zafi."

Yalcinkaya ya ce tsarin TOI-5799 ya bambanta saboda yana ɗauke da tauraron da ke da sababbin exoplanets biyu, TOI-5799b da TOI-5799c, dukkansu kusan kashi 70 cikin ɗari mafi girma fiye da Duniya kuma mai yiyuwar kasancewa duniyoyin dandaryar ƙasa ne.

Yayin da TOI-5799b ke juyawa kusa da tauraruwarsa kuma saboda haka tana da zafi, TOI-5799c tana cikin yankin da za ta iya tallafa wa rayuwa na tauraron kuma tana kammala zagayawa kowane kwanaki 14.

"Duniyar na wani waje mai nisa inda ruwa zai iya kasancewa a matsayin ruwa saboda zafin samanta na kusan digiri 63 na Celsius, amma yanayin zai iya canza abubuwa saboda ba mu san irin yanayin ta ba," ya ce.

"Za ta iya kasancewa mafi zafi sosai fiye da yadda ake zato ko kuma ya fi sanyi, ba mu sani ba tukuna."

"Idan akwai rayuwa a can, watakila akwai wasu alamun halitta (biosignatures) a cikin yanayinta, za mu iya nazarin hakan a nan gaba don ganin ko akwai rayuwa ko babu," ya lura.

"Rayuwa na iya wanzuwa a kan yawancin duniyoyi, amma idan akwai rayuwa a 'TOI-5799c', zai yiwu a gano hakan."