| Hausa
’Yan Haiti na murna saboda El Salvador ta hare-hare
Duniya
’Yan Haiti na murna saboda El Salvador ta hare-hare
A watan jiya, Bukele ya tura dakaru kusan 2,500 zuwa Haiti, bayan wasu ma’aikatan Majalisar Ɗinkin Duniya huɗu ’yan El Salvador sun fuskanci hari tare da ɓacewa a ranar 18 ga Oktoba.
 

Dubban mutane ne suka fito kan titunan babban birnin Haiti domin nuna goyon baya da yabawa ga Shugaban El Salvador, Nayib Bukele, da dakarunsa, waɗanda suka kai hare-hare kan gidajen wasu shugabannin ƙungiyoyin masu aikata laifuka da ke iko da yankuna daban-daban na ƙasar.

A watan jiya, Bukele ya tura dakaru kusan 2,500 zuwa Haiti, bayan wasu ma’aikatan Majalisar Ɗinkin Duniya huɗu ’yan El Salvador sun fuskanci hari tare da ɓacewa a ranar 18 ga Oktoba. Rahotanni sun ce Shugaban Amurka Donald Trump ya amince da tura dakarun, kuma a yayin wata tattaunawa ta wayar tarho, ya gaya wa Bukele cewa zai iya yin duk abin da ya ga ya dace.

Dakarun da ke yaƙi da ƙungiyoyin masu aikata laifuka a Haiti a halin yanzu sun haɗa da ’yan sandan ƙasar da sojojinta, da rundunar yaƙi da ƙungiyoyin masu aikata laifuka da Majalisar Ɗinkin Duniya ke mara wa baya, da wasu fararen hula da suka ɗauki doka a hannunsu ba tare da izini ba, da kuma kamfanin tsaro mai zaman kansa na Vectus Global, wanda Erik Prince, tsohon sojan kundumbala na Amurka, kuma wanda ya kafa shahararren kamfanin tsaro mai cike da ce-ce-ku-ce na Blackwater.

Ƙungiyar International Crisis Group ta yi gargaɗin cewa hukumomin Haiti ba su da wata dabarar da za ta ba su damar gano manyan barazanar da suka fi buƙatar samun kulawa, dd daidaita ayyukan hukumomin gwamnati, da kuma kawo ƙarshen tashin hankalin ta hanya mai dorewa.

Ƙarin Bidiyoyi
Tsokaci kan dambarwa tsakanin Gwamna Abba da matarsa Zainab
Musulunci zai zama addini mafi yawan mabiya a duniya nan da shekara tara
Dalilai 3 na dawowar Ronaldinho buga tamola
Tayin Isra'ila na dala 3,500 ga 'yan'Afirka mazauna kasar
Matsalar tsaro na ci gaba da zama muhimmin batu a zaben Nijeriya na 2027
Mulki wahala ne da shi, Allah-Allah nake na miƙa wa wanda zai gaje ni- Zulum
Karuwar hare-haren siyasa gabanin zabukan Nijeriya na 2027
‘Samar da ci gaba ne hanyar da za a kawo karshen ta’addanci a Afirka’
‘Ba ma jin tsoron Atiku, ba mu Kwankwaso yake yi wa aiki ba’
An gano matashi dan Australia da ransa bayan kwana shida