Hukumar kula da alhazai ta Nijeriya, Nahcon, ta yi karin haske kan batun da ake yi cewa kowane maniyyaci zai kara dala 100 a cikin kudaden da zai biya na aikin Hajji.
Tun da farko kamfanonin jiragen sama ne suka bukaci karin dala 250 kan kowane maniyyaci saboda sauya hanyar da za su yi zuwa Saudiyya don kauce wa bi ta Sudan skamakon yakin da ake yi a kasar.
Sauya hanyar za ta sa tafiyar ta kara tsawo daga Nijeriya zuwa Saudiyya.
A wata sanarwa da hukumar ta Nahcon ta fitar ranar Litinin, ta bayyana cewa “Duka jiragen alhazai za su bi wasu hanyoyi na daban wadanda za su kara tsawon tafiyar daga awa 1 da minti 40 zuwa awa uku, ya danganta daga wurin da jirgin ya tashi daga Nijeriya.
“Wadannan hanyoyin za su tilasta wa jiragen su bi ta sararin samaniyar Kamaru da Jamhuriyyar Tsakiyar Afirka da Uganda da Kenya da Habasha da Eritiriya,” in ji sanarwar.
Hukumar ta ce sauyin hanyoyin zai kara kudin man jirgin da sauran kudaden da suka shafi sufuri.
Nahcon ta kara da cewa hakan ne ya sa kamfanonin jiragen suka bukaci karin dala 250. Hukumar ta ce bayan ta yi nazari tare da masu ruwa da tsaki kan harkar sufurin jirigin sama a Nijeriya, ta cimma matsaya kamar haka:
- Hukumar ta bukaci gwamnatin tarayya ta amince ta yafe kashi 35 cikin 100 na kudin hukumomin sufuri domin jiragen sama wanda zai zama dala 55. Wannan zai rage karin kudin sufurin kan alhazan.
Tun a baya gwamnati ta zaftare kashi 65 cikin 100 domin rage kudin aikin Hajji. Bayan cimma wannan matsaya, dala 250 din da jiragen suka bukata ta koma dala 55.
- Sauran dala 195 din za ta kasance maniyyata 75,000 ne za su biya ta inda aka kiyasta kowane maniyaci zai biya dala 117.
- Domin biyan dala 117 din ba tare da kara dora nauyi kan alhazan ba, hukumar ta yanke shawarar cire kudin daga guzurin maniyyatan da hukumar za ta ba su na dala 800 inda za a mayar da shi dala 700.
- Sauran dala 17 din kuwa hukumar ta alhazai ta ce za ta bukaci kamfanonin jiragen saman su kara yin rangwame ga maniyyatan wadanda su ma yakin Sudan din ya shafe su.