Shugaban Amurka Joe Biden ya karbi baƙuncin shugaban Kenya William Ruto a fadar White House da ke birnin Washington. / Hoto: Reuters  

Ana sa ran shugaban kasar Amurka Joe Biden zai ayyana ƙasar Kenya a matsayin babbar ƙawar ƙungiyar tsaro ta NATO a ziyarar aikita kwanaki uku da shugaban Kenya William Ruto ya kai ƙasar.

Ruto wanda ya samu tarba daga Biden a fadar White House gabanin soma ziyararsa a ranar Alhamis, wadda za ta fara da faretin girmamawa kana ta ƙare da cin abinci na alfarma da daddare.

Ƙasar Kenya ce ta zama ƙasa ta farko a yankin kudu da hamadar Sahara da za ta samu wannan muƙami, lamarin da ke nuni da yunƙurin Washington na ƙarfafa dangantaka da ƙasar ta gabashin Afirka, wadda ta daɗe tana alaƙa ta kut da kut da Rasha da China, kana ta tura dakarunta 1,000 zuwa Haiti a matsayin wani ɓangare na rundunar da aka tura don magance matsalar tsaro a yankin Caribbean ƙarƙashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya.

Sauran ƙasashen da ake sa ran za su marawa sojojin Kenya baya sun hada da Bahamas da Barbados da Benin da Chadi da kuma Bangladesh.

Amurka ce ke ba da wannan matsayin ga ƙawayenta na kusa waɗannan ba mambobi ba ne a ƙungiyar NATO, waɗanda suke da alaƙar aiki da sojojin Amurka.

Gagarumin naɗi

A watan Maris ne Biden ya ayyana Qatar wacce ba ta cikin ƙungiyar NATO a matsayin babbar ƙawar Amurka, yana mai cika alƙawarin da ya yi Qatar a farkon shekarar.

"Ba zan iya kwatanta hanyar da ta fi dacewa a fara wannan ziyarar ba," in ji Biden a yayin soma taron shugabannin da masu fasaha.

''Mutanenmu sun kawo mana ci gaba tare da sanya mu a tsawun farko wajen samar da sabbin fasahohi da ke sauya rayuwar miliyoyin mutane. Ina nufin, a zahiri miliyoyin rayuka. kuma za mu wuce matsayin nan gaba.''

Amintacciyar ƙawa

Gyude Moore, Shugaban Shirin Afirka a Cibiyar Samar da ci Gaba a Duniya, ya ce Kenya ta tabbatar da kasancewarta amintacciyar ƙawar Amurka a daidai lokacin da Afirka ta Kudu ta aiwatar da manufofinta na ƙashin kanta kan ƙetare.

Cameron Hudson, wani jami'i a Cibiyar Kula da Dabaru da Ilimin Ƙasa da Ƙasa, ya ce matakin zai samar da wani sauyi da zai sa Kenya ta ''ƙara matsawa kusa da sararin samaniyar Amurka'' a 'yan shekaru, cikin har da ƙara ƙarfin haɗin gwiwa kan Somaliya.

"Yana da matuƙar muhimmanci domin babu wata ƙasa da ke kudu da hamadar Sahara da ke da wannan matsayi," in ji shi.

Amurka ta daɗe tana dogaro kan abokan hulɗarta na yankin Afirka amma dangantakar ta yi tsami da wasu muhimman ƙasashe, a cewar Hudson.

Ƙawayen nahiyar

Afirka ta Kudu ta fusata Amurka bayan da ta ki tsoma baƙi a takunkuman da aka ƙaƙabawa Rasha bayan mamayar da ta yi wa Ukraine da kuma gabatar da ƙara kan yaƙin kisan ƙare dangi da Isra’ila ke yi a Gaza.

Habasha ta rasa samun tagomashin Amurka saboda mummunan rikicin da ya ɓarke a yankinta na Tigray, yayin da Nijeriya, ƙasa mafi yawan al'umma a Afirka, ke fama da tashe-tashen hankula na cikin gida.

"Don haka Kenya tana tsaye ne ita kadai a yanzu, ina ganin, a tsakanin manyan ƙasashen yankin da Amurka za ta iya dogaro da su," in ji Hudson.

TRT World