Jama'a da dama ke jiran jin hukuncin da kotun za ta yanke a ranar Laraba. Hoto/Others

Alkalan da ke shari'a kan zaben gwamnan Kano a Nijeriya sun soma karanto hukunci daga wani wuri na daban da harabar kotun sauraren kararrakin zaben.

A yau Laraba ne Kotun take yanke hukunci kan zaben gwamnan jihar Kano na 2023.

Sai dai alkalan ba su je kotun ba, maimakon hakan sun soma yanke hukunci ta manhajar Zoom daga wani wuri.

Lauyoyi da wakilan jam'iyyun APC da NNPP sun kwashe tsawon lokaci a cikin kotun suna jiran zuwan alkalan amma ba su hallara ba. Amma suna jin bayanan alkalan daga cikin kotun.

A baya alkaliyar kotun ta yi zargin cewa wasu lauyoyi sun yi tayin ba ta cin-hanci domin ta sauya hukuncin da za ta yanke a zaben jihar ta Kano.

Jam'iyyar APC, wadda tsohon Mataimakin Gwamnan Kano Nasiru Yusuf Gawuna ya yi takara a karkashinta ce ta kai karar Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP kan rashin gamsuwa da sakamakon zaben gwamnan jihar.

A yayin zaben da aka gudanar a watan Maris din 2023, Abba Kabir Yusuf ya samu kuri’u 1,019,602 yayin da Nasiru Yusuf Gawuna ya samu kuri’u 890,705.

Ana cikin zaman dardar a Kano tun bayan da aka sanar da ranar da za a yanke hukuncin.

Tun kafin a sanar da ranar, magoya baya daga duka bangarorin sun rinka zanga-zanga inda suke neman kotun ta yi wa kowa adalci.

Sakamakon wannan hukuncin da za a yanke a ranar Laraba, tuni hukumar ‘yan sandan Nijeriya reshen Jihar Kano ta ce ta dauki matakai domin dakile duk wata tarzoma da kan iya barkewa bayan sanar da hukuncin kotu.

TRT Afrika