Yadda daliban da suka baro Sudan suke kallon shirin gwamnatin Nijeriya na tallafa wa karatunsu

Yadda daliban da suka baro Sudan suke kallon shirin gwamnatin Nijeriya na tallafa wa karatunsu

Batun sanin makomar karatun daliban da aka ceto daga Sudan shi ne abin da ya fi ci wa daliban da iyayensu tuwo a kwarya.
Batun sanin makomar karatun daliban da aka ceto daga Sudan shi ne abin da ya fi ci wa daliban da ma iyayensu tuwo a kwarya. / Hoto: AFP

Daga Mazhun Idris

Wasu daliban Nijeriya da aka ceto daga kasar Sudan sakamakon rikicin da ya barke a can, sun yi maraba da tsarin da gwamnatin kasar ta zayyana na shirin tallafa musu don kammala karatunsu a Nijeriya ko kuma a kasar Masar.

Ofishin jakadancin Nijeriya da ke Masar ne ya fitar da daya daga cikin wadannan shirye-shirye, inda zai hada-gwiwa da Babban Ofishin Kula da Daliban Kasa-da-Kasa na Ma’aikatar Ilimi ta Masar, don mayar da daliban na Nijeriya zuwa jami’o’in Masar.

An nemi daliban su gabatar da rahoton jarrabawa da shekarun karatu da suka kammala zuwa yanzu da hoton fasfo da lambar waya da kuma imel, gabanin bude shafin rajistar dalibai masu sauya makaranta na kasar.

Amma wata daliba da TRT Afrika ta tuntuba wadda ba ta amince a ambaci sunanta ba, ta ce har zuwa yau ba su samu wata gayyata a hukumance ba kan wannan shiri na gwamnati, wa lau na mayar da su Masar ko na tura su jami'o'in gida Nijeriya.

Su ma wasu iyayen daliban da TRT Afrika ta zanta da su, sun tabbatar da cewa har zuwa yanzu ba a tuntube su ba, kuma ba a yi shawara da su ba kan yadda yaransu za su ci gajiyar wannan dama.

Wani mahaifin daya daga cikin daliban, Malam Aliyu Musa Giade, ya ce sun ji dadin labarin wannan kokari da gwamnati ke yi don ganin karatun da ‘ya’yansu suka fara a Sudan bai tafi a banza ba.

Ya ce “Yarona yana cikin wadanda aka dawo da su Nijeriya ranar 9 ga watan Mayu, inda ya baro jami’ar International University of Africa, inda yake karanta kimiyyar kwamfuta, a aji na biyu. Shekara biyu suka rage wa dana ya kammala digirinsa”.

Batun sanin makomar karatun daliban da aka ceto daga Sudan shi ne abin da ya fi ci wa daliban da ma iyayensu tuwo a kwarya.

Ita ma shugabar hukumar kula da ‘yan Nijeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa, ta ce ta yi ta samun kiran waya daga iyaye da dalibai, kan sanin hanyoyin da dalibai za su kammala karatunsu a Nijeriya.

A wani bangaren, tun a ranar 10 ga watan Mayun nan ne hukumar share-fagen shiga jami’a ta JAMB ta tabbatar da cewa daliban da suka dawo daga Sudan za su iya kammala karatunsu a gida Nijeriya.

An ruwaito shugaban na JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede yana cewa hukumar tasa za ta bayar da duk tallafin da ya dace don ganin daliban sun iya kammala karatunsu a jami’o’in Nijeriya idan suna so.

A makon nan aka jiyo Dokta Nasir Sani Gwarzo, babban sakataren ma’aikatar jin-kai kuma shugaban ofishin kula da ceto ‘yan Nijeriya daga Sudan, yana cewa an kammala kwaso dalibai 2,518, bayan yin zango a kasashen Saudiyya, da Chadi, da Habasha.

An gudu ba a tsira ba

Mahaifin daya daga cikin daliban ya nuna takacin cewa tun a farko da ma sun zabi biyan makudan kudi don yaransu su je makarantun kasashen waje ne, domin gujewa rashin tabbas da karatu yake da shi a jami’o’in Nijeriya mallakar gwamnati.

Ya ce abin da suka guda yanzu shi zai faru, matukar ba jami’o’i masu zaman kansu yaran nasu suka shiga ba a Nijeriya.

“Ba a san sanda rikicin Sudan zai zo karshe ba, balle a yi tunanin yiwuwar komawar dalibai can, don kammala karatu.

Dangane da mayar da yaransu kasar Masar, mahaifin ya yi nuni da zullumin da suka shiga lokacin da ‘ya’yansu suke tsakiyar rikicin Sudan din. Ya ce tuni wasu iyayen yara suka sha alwashi ba za su kara tura ‘ya’yansu kasashen waje ba don yin karatu.

Gwamnatin Nijeriya ta sanar da cewa za a hada gwiwa tsakanin hukumar JAMB da hukumar kula da jami’o’i ta kasa, wato NUC, don tabbatar da daliban su samu gurbin kammala karatun nasu, ba tare da wata matsala ba.

Wasu iyayen sun nuna cewa zai yi kyau gwamnati ta tallafa musu da kudi, saboda wasu sun riga sun biya kudin makarantar yaransu, kuma sun kashe makudan kudi a kokarin ganin 'ya’yansu sun komo gida.

Wannan ne ya sa ma da yawansu ba za su iya kai ‘ya’yansu wasu kasashe kamar Masar ba, kasancewar “jami’o’in Masar suna da tsada”.

Sakamakon irin wannan yanayi da dalibai da iyayensu suka shiga, an ruwaito wata jami'a mai zaman kanta a kudancin Nijeriya tana yi wa daliban da suka baro Sudan tayin ragin kudin makaranta idan suka zabi kammala karatunsu a jami'ar.

Kakakin Jami'ar Fountain University, da ke birnin Osogbo na jihar Osun, Taoheed Alimi, ya ce jami'ar ta fitar da wani tsari don tallafa wa dalibai da iyayen da rikicin Sudan ya shafa. Jami'ar ta samar da gurabai ga daliban.

Tsawaita shekarun karatun dalibai

Wasu daliban da TRT Afrika ta tuntuba, sun koka kan cewa har a halin yanzu ba su gama farfadowa daga fargaba da rashin tabbas da suka shiga a Sudan ba, da tararrabin makomar karatunsu, kuma a yanzu jikinsu ya yi sanyi.

To yanzu yaya kuma za su ji idan suka samu kansu a jami’o’in gwamnati a Nijeriya, ganin yuwuwar samun tsaikon daga yajin aikin malamai, ko kuma wasu matsalolin da ke iya shafar daliban makarantun gwamnati a kasar?

Rahotanni sun nuna daga cikin daliban akwai wadanda suke zango na karshe na kammala karatunsu kafin rikicin ya tilasta musu gudowa daga Sudan.

Ko idan daliban suka samu damar cigaba da karatun nasu a jami’o’in Nijeriya, hakan zai tsawaita shekarun da ya kamata su kammala karatun, musamman wadanda suka riga suka yi nisa a karatunsu?

Sanarwar shugaban na JAMB ta ce don biyayya ga Shelar Arusha/Addis Ababa, duk dalibin da ya yi kaura zuwa wata jami’ar dole ne ya kwashe akalla shekara biyu a duk jami’ar da ya zaba kafin ya samu takardar shaidar kammala jami’a.

Duk da JAMB ta ce kowane dalibi yana da ‘yancin zabar makarantar da zai kammala karunsa a Nijeriya, hukumar ta ce dole daliban su kawo bayanin sakamakon jarrabawarsa na shekarun baya, wanda zai iya yi wa wasu daliban wuyar nemowa.

Baya ga tayin gwamnatin Nijeriya, akwai rahotannin da suke nuna cewa wasu jami’o’i a Masar sun bude kafofinsu ga daliban na Nijeriya da suka yi gudun hijira daga Sudan, har ma da Ukraine.

Amma dai alamu sun fi nuna cewa za a samu dalibai da dama da za su zabi kammala karatunsu a jami’o’in cikin gida, maimakon sake fita kasashen waje don neman ilimi.

TRT Afrika