Janar Abdourahmane Tiani ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasa bayan sojoji sun kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum a watan Yuli./Hoto: Fadar Shugaban Kasar Nijar.

Wata Kotun Yammacin Afirka ta yi fatali da karar da sojojin Nijar suka shigar a gabanta inda suka nemi ta tursasa wa kungiyar ECOWAS ta dage takunkuman da ta sanya musu.

Sojojin sun kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum ranar 26 ga watan Yuli sannan suka tsare shi da iyalinsa a gidansa da ke fadar shugaban kasar.

Hakan ne ya sa kungiyar ECOWAS ta kakaba musu jerin takunkumai ciki har da rufe iyakokinsu da kuma katse lantarkin da Nijeriya ke bai wa kasar, abin da ya jefa ‘yan kasar cikin karancin abinci da magunguna da sauransu.

Sai dai kotun ta ce sojojin ba su da ikon shigar da kara a madadin Jamhuriyar Nijar.

Labari mai alaka: Sojojin Nijar sun yanke huldar soji da Benin

"Ba a amince da sojojin a matsayin gwamnati ba kuma su ba mambobi ne na ECOWAS don haka bukatarsu ba ta da karfi.Kuma na yi watsi da ita", in ji Mai Shari’a Dupe Atoki.

A watan Oktoba gwamnatin sojin Nijar ta ce za ta zaftare yawan kudin da take shirin kashewa da kashi 40 cikin dari saboda takunkuman da aka sanya wa kasar tun da sojoji suka kwace mulki, a wani yanayi na irin matsin tattalin arzikin da ta fada a ciki.

Nijar ta kwashe shekaru tana kawance da kasashen Yammacin duniya, ciki har da Amurka, a yaki da masu tayar da kayar baya wadanda suka kashe dubban mutane.

Sai dai gwamnatin sojin Nijar ta soke yarjejeniyoyi da dama da ta kulla da Tarayyar Turai da kuma Faransa.

TRT Afrika da abokan hulda