Nijar na kokarin zamanantar da kauyukan kasar da waya da intanet

Nijar na kokarin zamanantar da kauyukan kasar da waya da intanet

Kauyuka 2,075 ne za su ci moriyar shirin a zagayen farko cikin wata 36.
Shugaban kasar Nijar ya ce shirin na son zamanatar da kauyukan tare da inganta rayuwar mazauna kauyukan/Hoto:Facebook/Mohamed Bazoum

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar tana son ta samar wa ‘yan kasar miliyan uku da ke zama a kauyuka intanet da layin waya a cikin wani shirinta na zamanantar da kauyukanta

Shugaban kasar, Mohamed Bazoum ne ya wallafa sanarwar wannan gagarumin shiri a shafinsa na Twitter.

Sanarwar ta ce gwamnatin na wannan aiki ne domin inganta rayuwar mutanen karkara baya ga zamanantar da kauyuka.

Kauyuka 2,075 ne za su ci moriyar shirin a zagayen farko cikin wata 36.

A Jihar Maradi, kauyuka 634 ne za su ci moriyar shirin yayin da kauyuka 504 za su ci moriyarsa a Jihar Zinder, ita kuwa Jihar Tahoua kauyukanta 487 ne ke cikin shirin.

Jihar Tilleberi na da kauyuka 259 yayin da Jihar Dosso ke da kauyuka 228 cikin kauyukan da za su amfana da shirin.

Dubban kauyuka ne za su ci moriyar shirin a jihohin kasar / Hoto: Facebook/Mohamed Bazoum

A Jihar Diffa, kauyuka 45 ne ke cikin shirin yayin da Jihar Agadez ke da kauyuka 16 a cikin shirin, kuma ita Jihar Niamey ke da kauyuka biyu a cikin shirin.

An hada sanarwar da wani bidiyo da ke nuna bayanai game da yadda mutanen wasu daga cikin kauyukan suka karbi aikin na gwamnatin kasar.

Gwamnatin tana fatan wanan aikin zai inganta rayuwar marasa galihu a kasar da ake ganin tana cikin kasashen da suka fi fama da talauci a duniya.

TRT Afrika da abokan hulda