Har yanzu akwai ruɗani a tattare da ma'anar hukuncin, wanda kotun ta yanke ta manhajar 'Zoom' a ranar Alhamis

An shiga ruɗani kan ainihin hukuncin da Kotun Sauraron Kararrakin Zabe ta yanke a kan shari'ar zaben gwamnan Jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Nijeriya.

Har yanzu akwai ruɗani a tattare da ma'anar hukuncin, wanda kotun ta yanke ta manhajar 'Zoom' a ranar Alhamis, kan ƙarar da tun farko dan takarar gwamna na Jam'iyyar PDP Isa Ashiru ya shigar yana kalubalantar zaben Uba Sani na Jam'iyyar APC.

Bayan kammala hukuncin da alkalai uku karkashin jagorancin Mai shari'a Victor Oviawe suka yanke ne sai wasu rahotanni suka ce Kotun sauraron kararrakin zaben ta tabbatar da nasarar Uba Sani a matsayin zababben gwamnan jihar a zaben watan Maris na 2023.

A bangare guda kuma wasu rahotannin suka ce kotun ta ayyana zaben ne a matsayin wanda bai kammala ba (Inconclusive), ta hanyar soke nasarar Uba Sani.

Wadannan al'amura biyu sun jefa mutane a ruɗani musamman ganin dukkan lauyoyin bangarorin ma akan matsaya biyun suke tafiya, kowa na ɗaukar hukuncin da ya yi wa ɓangarensa daɗi.

Yaya waɗannan jam'iyyu biyu suka dauki hukuncin?

Daya daga cikin lauyoyin da ke kare Uba Sani na APC, Barista Sunusi Musa SAN, ya ce hukuncin kotun na nufin bangarensu ne ya yi nasara saboda wasu dalilai da ya bayyana.

"A watan Yuni muka nemi kotu da ta kori wwannan ƙarar saboda su waɗanda suka shigar ɗin sun yi watsi da ƙarar tasu saboda akwai wasu abubuwan da suka dace su yi amma ba su yi ba," in ji lauyan.

"To amma saboda doka ta hana kotu ta kori ƙarar a wannan lokacin sai dole an zo an saurare ta a ƙarshe a faɗi ma mene ne hukuncin nata, kotun ta yarda da mu cewa tun ranar 31 ga watan Mayu su masu ƙarar sun yi watsi da ita, don haka yanzu kotu ta ce ta kori wannan ƙarar.

"Amma sai kotun ta ce ko da za a je kotun gaba a ce wannan abin da ta yi ba haka ba ne, to a ganinta kamata ya yi a ce sai an yi zaɓe a wasu akwatuna 22, sannan a samu wanda ya ci zaɓe, amma a yanzu yadsa sakamakon zaɓe yake ta bar shi a haka, APC ta fi PDP da ƙuri'u 11,000, amma a je a sake zaɓe a waɗannan akwatunan don tabbatar da wanda ya ci zaɓe," in ji Sunusi Musa a wani bidiyo da aka wallafa a Facebook.

Amma a nasa ɓangaren, Barista Baba Lawal Aliyu, lauyan Isa Ashiru ya gaya wa manema labarai cewa hukuncin da kotu ta yanke na nufin a sake zabe a mazabu goma sha hudu na kananan hukumomi guda hudu.

A cewarsa " Alkalai uku ne suka yi shari'a - biyu su ne masu rinjaye, inda suka amince a sake zabe a kananan hukumomi hudu, yayin da alkali daya ya tabbatar da Uba Sani a matsayin gwamna".

Jim kaɗan bayan yanke hukunci dukkan jam'iyyun biyu APC da PDP sun fitar da sanarwa inda ita APC ke murna da hukuncin kotun na tabbatar da Uba Sani, yayin da PDP kuma take nuna gamsuwarta kan sake zabe a akwatunan da aka bayyana.

Yadda zaman kotun ya wakana

Kotun ta cika maƙil da lauyoyi da 'yan jarida da safiyar Alhamis inda aka sanya kyamarori da wasu na'urori ta ko'ina a cikinta, amma daga bisani sai alkalan suka bayyana ta mahajar 'Zoom' suka soma karanta hukunci kan karar.

An tsaurara tsaro a sassan jihar ta Kaduna musamman a cikin birnin sakamakon zaman dar-dar da ake yi gabanin hukuncin kotun.

A watan Maris aka gudanar da zaben gwamnonin Nijeriya inda a Kaduna babban jami'in hukumar zabe Farfesa Lawal Suleiman Bilbis ya ayyana Uba Sani a matsayin wanda ya yi nasara inda ya samu kuri'a 730,002, yayin da dan takarar da ke biye da shi Isa Ashiru ya samu kuri'a 719,196.

Sai dai Isa Ashiru ya garzaya kotu yana zargin cewa an tafka magudi a zaben.

Tun daga wancan lokacin ake tafka shari'a kuma lauyoyin bangarorin biyu suka gabatar da hujjjojinsu a gaban alkalan da ke sauraren karar.

Alkanan na yanke hukunci ta hanyar 'Zoom' ne a yayin da ake zaman dar-dar a Kaduna./TRT Afrika
TRT Afrika