Rahotannin sun ce dukkan bangarorin biyu na jam’iyyar NNPP mai mulkin jihar da APC mai kalubalantar sakamakon zaben ne suka gudanar da zanga-zangar./Hoto: Premier Radio

Dumbin jama’a sun gudanar da zanga-zanga a kan titunan birnin Kano da ke arewacin Nijeriya a daidai lokacin da kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar ke zamanta a ranar Litinin.

Masu zanga-zangar sun ce sun fita ne don neman a yi adalci kan shari'ar zaben, wacce zargin kokarin bai wa alkalan da ke shari'ar cin-hanci ya dabaibaye ta.

Tun da fari a ranar Litinin din rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta fitar da sanarwar cewa ta haramta yin zanga-zanga a ranar sauraron karar, amma ga alama mutane sun bijire wa umarnin.

Rahotannin sun ce dukkan bangarorin biyu na jam’iyyar NNPP mai mulkin jihar da APC mai kalubalantar sakamakon zaben ne suka gudanar da zanga-zangar.

Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Kano CP Muhammad Usaini Gumel ya ce sun samu bayanan sirri cewa wasu mambobin jam’iyyun siyasa na APC da NNPP sun dauko hayar wasu mutane don yin zanga-zanga a jihar.

Rundunar ta ce ba za ta lamunci duk wani yunkuri na kawo tarnaki ga zaman lafiyar Jihar Kano ba.

Zargin cin hanci da neman sauya hukunci

A ranar Talata 18 ga watan Agusta ne daya daga cikin alkalan da ke sauraron kararrakin zaben, Mai Shari’a Flora Ngozi Azinge ta yi zargin cewa wasu lauyoyi suna neman su sayi alkalan ta hanyar ba su cin-hanci da kuma neman su sauya hukuncinsu.

Sai dai Mai Shari’a Azinge ba ta fadi bangaren da ya tunkari alkalan da batun bayar da cin-hancin ba.

Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce sosai a fadin jihar da ma wajenta, in da har kungiyar lauyoyi ta Jihar Kano ta nemi mai shari’ar da ta bayyana sunayen lauyoyin da suka yi hakan domin ta dauki mataki.

APC na neman kotun ta tabbatar da Gawuna a matsayin gwamna yayin da NNPP da INEC ke neman kotu ta yi watsi da karar: Hoto: OTHERS

Yayin kammala zaman kotun na Litinin Mai Shari’a Oluyemi Akintan-Osadebay, shugaban tawagar alkalan uku, wanda ya yi alkawarin yi wa dukkan bangarorin adalci, ya ce za su yanke hukunci kafin cikar kwana 180 na wa’adin da doka ta tanada.

An kawo karshen zaman ne bayan da dukkan bangarorin biyu suka yi jawabi, inda APC ta nemi kotun ta tabbatar da Nasir Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Kano, yayin da INEC da NNPP kuma suka nemi kotun da ta yi watsi da wannan kara.

Zaman kotun na farko

Tun da fari a lokacin zaman shari’ar na farko a watan Yuni APC, wacce ita ke kalubalantar zaben, ta ce tana da shaidu fiye da 300 da za ta gabatar wa kotun.

Sannan a wani zama da ta yi, kotun ta bai wa jam'iyyar damar duba na’urorin BVAS da hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ta yi amfani da su a zaben gwamnan da aka yi ranar 18 ga watan Maris na 2023.

Tawagar alkalan mai mutum uku ta bai wa wanda ya shigar da korafin damar duba BVAS din da aka yi amfani da su a kananan hukumomin Bebeji da Gezawa da Tudun Wada da Garko da Ungogo da Ajingi da Bunkure da Warawa da kuma Karaye.

TRT Afrika