Shugaban Nijeriya Tinubu zai ƙaddamar da tashoshin sarrafa iskar gas uku a ƙasar

Shugaban Nijeriya Tinubu zai ƙaddamar da tashoshin sarrafa iskar gas uku a ƙasar

An kulla yarjejeniyar ne don rarraba makamashin iskar gas mafi tsafta da inganci ga masana'antu a jihar.
An kulla yarjejeniyar ne don rarraba makamashin iskar gas mafi tsafta da inganci ga masana'antu a jihar. Daddy O X

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu na shirin kaddamar da wasu masana’antun sarrafa iskar gas guda uku wadanda za su bunkasa samar da iskar gas ga kasuwannin cikin gida na ƙasar zuwa kubik miliyan 500 a kowace rana, tare da kuma inganta zuba jari a kasar.

Ayyukan, waɗanda Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPCL) da abokan hadin gwiwa ke gudanarwa, za a yi su ne don tallafa wa ƙoƙarin gwamnatin tarayya na inganta darajar ɗaga kadarorin iskar gas na ƙasa tare da rage hayaƙin ƙona iskar gas.

An bayyana hakan ne a ranar Juma’a a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale.

Ya bayyana cewa, an hanzarta kai ayyukan tun daga farkon gwamnatin Shugaba Tinubu wajen ɗorewar manufar zurfafa samar da iskar gas a cikin gida a matsayin hanyar bunkasa tattalin arziki.

Shell ya sa hannu kan yarjejeniyar bututun iskar gas na $100m da jihar Oyo

A wani labarin na daban kuma, Kamfanin Shell a Nijeriya ya sanya hannu kan wata yarjejeniya da jihar Oyo da ke kudancin kasar domin gina tsarin isar da bututun mai da zai yi hidima ga masana’antu a jihar kan kudi dala miliyan 100, kamar yadda gwamnatin Oyo ta bayyana a ranar Juma’a.

Yarjejeniyar da aka sanya wa hannu a Landan tare da Shell Nigeria Gas (SNG) na da matukar muhimmanci ga kokarin da jihar ke yi na bunkasa masana'antu da ci gaban tattalin arziki tare da inganta samar da wutar lantarki ga wuraren zama da masana'antu.

Gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde (a hagu) ya sanya hannu kan yarjejeniyar a Landan. Hoto / Oyo state

Aikin, wanda aka fara amincewa da shi a shekarar 2020, ya yi niyya ne don rarraba makamashin iskar gas mai tsafta kuma mafi inganci ga masana'antu a jihar ta hanyar rarraba gas mai yawan kusan kamu kubik miliyan 50 na iskar gas a kowace rana.

“Wannan aikin iskar gas na kimanin dalar Amurka miliyan 100, ya hada da gina tashar iskar gas (PRMS) da kuma shimfida bututun da SNG za ta yi. Bayan kammala aikin za a mayar da mallakarsa ga Jihar Oyo bayan shekara 20," in ji Oluseyi Makinde, gwamnan jihar Oyo a cikin wata sanarwa.

Kamfanin Shell Nigeria Gas Ltd, wanda aka kafa a shekarar 1998, yana gudanar da aikin watsa iskar gas da rarrabawa sama da kilomita 138 (mil 86) kuma yana hidima fiye da abokan ciniki 300 a cibiyoyin masana'antu a fadin jihohin kudancin NIjeriya.

TRT Afrika