Mahukunta na ci gaba da tonon gawarwaki yayin da adadin wadanda suka mutu ya karu. Hoto: Reuters

Daga Emmanuel Onyango

Har yanzu jama'a da dama a ciki da wajen kasar Kenya na cikin yanayi na firgici da tashin hankali, yayin da ake ci gaba da tono karin gawarwakin mutane bayan mutuwar da suka yi mai alaka da ayyukan wata kungiyar asiri a gundumar Kilifi da ke kudu maso gabashin kasar.

Lamarin, wanda ya fara fitowa fili a watan Afrilu, ya fi dimauta ‘yan uwan wadanda abin ya shafa da suka hada da mata da kananan yara – wadanda ake zargin shugaban kungiyar ya ba su umarnin su kashe kansu domin su ga Yesu.

"Ba mu taba ganin addinin da ke tilasta wa mata masu shayarwa da jarirai su yi azumi ba," in ji Zipporah Kwamboka, wacce tun shekarar 2021 ta yi wa 'yan uwanta maza ganin karshe, ta shaida wa TRT Afrika.

A wannan makon aka ci gaba da tono gawarwakin mutanen da ake zargi sun mutu sakamakon alaka da kungiyar asiri "mai kisa" a Kenya a kusa da dajin Shakahola, a karo na uku.

Wadanda suka mutu kawo yanzu sun haura mutum 250 bayan an gano wasu gawarwakin kusan 12 a ranar Talata, hukumomi na fargabar akwai wasu kari a wasu wuraren a babban dajin da ke kusa da garin Malindi ta gabar teku.

'Yan uwanta Zipporah maza sun bata tun bayan shiya kungiyar a shekarar 2021. Hoto: wasu

Alamu sun nuna cewa yunwa ce ta haddasa mutuwar, amma wasu da suka mutu - ciki har da yara – an ga alamun an shake su ko an rufe musu hanyoyin shakar iska, a cewar kwararrun likitocin da gwamnati ta nada wajen gudanar da bincike.

Jiran tashin hankali

‘Yan sanda sun yi imanin cewa gawarwakin na mabiyan Paul Nthenge Mackenzie ne, wani direban tasi da ya zama shugaban bishara na Cocin Good News International, wanda aka ce koyarwarsa tana sanya wata tsattsaurar akida ta son samun hanyar zuwa Aljanna.

Cikin hawaye, Kwamboka ta ce ‘yan uwanta maza sun sayar da kadarorin da suka mallaka kafin su shiga kungiyar asirin.

''Sun sayar da filin gidanmu sai suka ce za su sayi fili a wani waje da ke (makwabciyar) Tanzaniya. Sai kuma a wannan shekara cikin watan Afrilu muka samu labarin cewa su mambobi ne na Cocin Good News International,” in ji ta.

Kwamboka na daga cikin ‘yan uwan gomman mutanen da wannan lamari ya ritsa da su inda suka yi zaman dirshen suna jiran bayanai kan inda ‘yan uwansu suke.

Kungiyoyin asirai tare da koyarwar tsubbu a baya sun yi ta sanadin mutuwar mutane da dama tare da haifar da wasu wahallahu da mabiyansu ke fuskanta a wasu sassan Afirka.

Na baya-bayan nan da ya faru a Kenya, ana kyautata zaton shi ne ya fi muni a cikinsu duka a tarihin kungiyoyin asiri a nahiyar, ganin irin adadin mutane da kuma yanayin da mutanen suka rasa rayukansu.

Jami’ai sun ce galibin wadanda suka mutu, sun mutu ne saboda zargin zama da yunwa. Hoto: AA

A yanzu haka wata tawaga ta shugaban kasa ta fara aikin cike gibin yadda doka ta shardanta da kuma yadda al’umma ta bari Machenize ya yada koyarwarsa da ake zargin ta yi sanadin mutuwar daruruwan mutane.

A baya dai mai wa’azin ya yarda da yin wa’azin tsubbu. Duk da cewa ya gurfana a gaban kotu, har yanzu ba a bayyana hakikanin tuhumar da ake masa ba.

Jami'ai sun ce za a tuhumi Mackenzie da laifukan da suka shafi ta'addanci saboda amfani da ilimin addini wajen sauya tunanin dubban mutane.

Kafofin yada labarai na cikin gida a Kenya sun ruwaito cewa ya musanta aikata ba daidai ba dangane da yawan mace-macen da mabiyansa suka yi.

Mu'ujiza mai jan hankali

Ana tsare da Mackenzie, sannan hukumomi sun ce ana ci gaba da gudanar da bincike.

Limamin Cocin na amfani da tashar gidan talabijin dinsa, wanda ake kuma watsa shirye- shiryensa ta kafar Intanet wajen jan hankalin mabiyansa daga kasar ta kenya da makwabtanta, amma hukumomi sun ce wasu koyarwar tasa sun wuce hankali.

Ya sauya tunanin mabiyansa ta hanyoyi da dama wadanda suka yi imanin cewa sun yi aikinsu a duniya kuma za su samu ceto idan suka mutu, a cewar wadanda suka bar cocin.

Mummunan yanayin ya jefa al'ummar Kenya da dama cikin yanayi na damuwa game da yawan mutanen da suka shiga ayyukan kungiyar asirin da kuma yadda dokokin da ake da su a halin yanzu suka ba da dama da har aka gagara sanin abin da ke faruwa a dajin Shakahola na tsawon lokaci.

“Yawancin mutanen da za su tsinci kansu cikin wannan kungiyoyi suna fuskantar wani kalubale na rayuwa,” in ji James Mbugua, masanin ilimin halayyar dan adam a Jami'ar Nazarene ta Afirka, Jami'ar Addinin Kirista a Kenya.

'Yan uwan ​​wadanda suka mutu ta sanadiyar lamarin na kungiyar asirin suna neman amsa. Hoto: Reuters

"A halin da muke ciki musamman a nan Kenya, mafi yawan mutane na cikin yanayi na kuncin rayuwa.. shi ya sa idan suka ji abubuwa na al’ajabi, nan take suke bin ire-iren wadannan kungiyoyin.

"Wadanda koyarwarsu ke nuni da cewa wurin da suke yafi inda mutum yake kyawu,” in ji shi.

Daga cikin batutuwan da kwamitin shugaban kasa zai mayar da hankali a kai shi ne batun 'yancin addini, wanda dokokin Kenya suka tanada, amma da dama a yanzu suna ganin ana wuce gona da iri.

Kenya kasa ce da ke da mabiya da suka yi imani da addini - kashi 85 daga cikin 100 Kiristoci ne yayin da kashi 11 cikin 100 Musulmai ne bisa kiyasin hukumar kasa.

Daukar mataki

Shugaban kasar Kenya William Ruto ya yi Allah wadai da yanayin da ya janyo asarar rayukan jama'a tare da shan alwashin cewa gwamnatinsa za ta dauki mataki bayan amincewa da gazawar hukumomin kasar wajen sa ido kan ayyukan kungiyoyin asiri.

Ana ci gaba da kiraye-kirayen a samar da doka da za ta duba tsarin ayyukan kungiyoyin addinai da shugabanninsu.

Wasu sun ba da misali kan irin nasarorin da aka samu a Rwanda da irin wannan doka, wadda a karkashinta dole ne malaman addinai su kai wasu wasu matakai na samun ilimi kuma su ci jarabawar da za ta sa su cancanta.

Yayin da duk wani tallafi da sauran gudunmowar kudi da kungiyoyin ke samu dole ne su shiga ta hanyar banki don tabbatar da bincike tsari mai kyau.

Shugaban cocin, Fasto Paul Mackenzie, yana hannun hukuma. Hoto: Reuters

Amma daidaita ayyukan da ke da alaka da addini na iya haifar da tashin hankali idan aka yi la'akari da yanayin da al’ummomi suka yi imani da addinai.

Masu nazari sun ce hakan zai zama babban kalubale ga kwamitin aiki na gwamnati a yunkurinsa na ganin an cimma matsaya kan shirin yin garambawul da zai kare ka’idojin koyarwa da ayyukan addinai masu cutarwa.

Masu goyon bayan hakan kuwa na ganin babu wani zabi da ya fi haka kyau. "idan muka yi magana game da sharudda ba wai muna magana ba ne game da hana yin ibada ba. Shugabannin addinai suna bukatar yin aiki cikin sharuddai da iyakoki,” in ji Dr Mbugua.

“Wannan lamari na Shakahola ya dade yana faruwa kuma mai yiwuwa zai iya yin muni sosai a nan gaba, ganin yadda ake yawan samun kungiyoyin addini a wannan lokaci. Muna bukatar mu fada wa kanmu gaskiya,” in ji shi.

Ga Zipporah Kwamboka da sauran ’yan uwan wadanda al’amarin ya shafa, abin da suka sa a gaba shi ne asamar samun adalci tare da karin amsa kan yarda da kuma dalilin da ya sa suka rasa ‘yan uwansu a cikin irin wannan yanayi na ban tausayi.

TRT Afrika