Rashid: Manomin Zanzibar mai dabarar da ke yakar karancin abinci

Rashid: Manomin Zanzibar mai dabarar da ke yakar karancin abinci

Rashid Rashid ne dan yankin Zanzibar kadai da ke yin noma a inda babu kasa.
Rashid Rashid a gonarsa. / Hoto: Reuters

Daga Charles Mgbolu

Zanzibar yanki ne da ke gabar Tekun Indiya a kasar Tanzania. Tsibiran yankin na da kyau sosai daga sama inda za ka hangi shudayen igiyar ruwa na motsi da kawata wuraren wanka.

Amma rayuwa a kasa kuma ta nesanta daga jin dadi, kamar yadda al'ummu da dama suka watsu a sassan Gabashin Afirka, suna gwagwarmaya da karancin abinci saboda yawaitar adadin jama'a da yawansu ya kai 800,000.

A shekarar 2006 fari da karancin ruwa ya lalata mafi yawan gonakin yankin masu girman sama da eka 10,000, kamar yadda MDD ta sanar.

Daga 2020 zuwa yau, yankin Gabashin Afirka ya fuskanci fari da karancin ruwan sama har zuwa karshen 2022. Ofishin Kula da Ayyukan Jin Kai na Majalisar Dinkin Duniya ya rawaito cewa lokacin damuna na watan Maris din 2022 ya kasance mafi samun karancin ruwan sama a shekaru 70 da suka wuce a kasar.

Tsananin karancin abinci

Wani nazari na baya-bayan nan da Majalisar Dinkin Duniya ta yi kan karancin abinci a Zanzibar ya bayyana cewa mutum 147,000 na fama da matsanancin karancin cimaka, saboda tashin gwauron zabi da farashin kayan abincin ya yi da rashin ruwan sama na lokaci mai tsayi.

Manoman yankin irin su Rashid Rashid sun yi tunanin yadda za su tsaya da kafufunsu. Yana yin noma a inda babu kasa a Zanzibar, dabarar noma a inda babu kasa.

Ya shaida wa TRT Afirka cewa "Hydroponic wata hanya ce ta yin noma da ruwa kawai ba tare da kasa ba. Muna shuga tsirrai na hatsi, kayan miya da sauran ganyayyaki inda muke amfani da takin kashin kifaye da muke tacewa."

"Tare da wannan tsarin noma, muna sabunta amfani da ruwa. Muna saka famfuna, wadanda suke zagaya wa da ruwan. Ruwan na tafiya ga tsirran sannan ya sake dawowa zuwa ga ma'ajiyarsa."

Dabarar noma ta Hydroponics na amfani da ruwa sosai da 'yar kasa kadan.

Kasar da aka kwashe

Wata sabuwar fasaha ce da ta zo tsibirin a lokacin da ya dace, wanda yanki ne da ba matsalar yanayi kawai yake fuskanta ba, har da ta karewar kasar da ake da ita.

"Abun takaici, kasar da muke da iya da yawa don yin noma ce mutane suka sare ta suka kwashe suna gina gidaje da sauran gine-gine. Wannan ya rage yawan gonakin noma a Zanzibar."

Rashid ya kara da cewa "Ya zama dole mu je yankunan da mutane ba sa yarda su noma, mu gyara wajen mu mayar da su gonaki."

Abu ne mai kyau ga manomi irin Rashid da ke bukatar waje kankani don yin noman da zai samu amfani da yawa.

Ya ce "A yanzu ina da dashe kusan 3,000 na ganyen latas a kowanne wata da ke girbewa a waje mai girman sukwayamita 200. Idan da ba na amfani da wannan dabara ta noma a inda babu kasa, da sai na yi amfani da waje da yake da girman ninki goma na wajen da na ke amfani da shi, domin smaun damar girbar wannan adadi."

Haduwa da dama

"Wannan abu ya faro ne a 2008 a lokacin da na yi aiki a wani gidan hotel a matsayin akawu, inda ga gibi a kayan marmari da kayan miya da ake kawo wa, musamman ga masu zuwa otel din.

"Amma a wannan lokaci, ban dauki shawarar ba har sai bayan kammala digiri na biyu a Jami'ar Dundee, Scotland inda na karanta kula da harkokin mai da iskar gas."

Rashid ya ci gaba da cewa "A nan ne na halarci azuzuwa na kyauta da suka ba ni haske wajen fara wannan nau'in noma, nan da nan na gano wannan ce amsar matsalar karancin abinci da kasata ke fuskanta."

Rashid ya kuma ce yana jin dadin yadda gonarsa ke ci gaba da habaka tana jan hankalin mutane, amma ya fi damu wa da yadda jama'a da yawa ba su fahimci amfanin wannan tsari na noma ba tare da kasa ba.

"Abun takaici a ce yadda shugabanni suke kallon wannan ci gaba a Zanzibar amma kuma su zauna haka su ki tallafawa."

Noma ba tare da kasa ba n a samar d aabinci da yawa saboda yadda manomi ke kula da shi a kodayaushe.

Yada sakonnin

Duk da haka, Rashid na aiki tukuru don yada wannan sako game da noma ba tare da kasa ba a wannan tsibiri.

Ya ce "Watakila wannan ne mataki mafi kyau da girma da za mu dauka game da kalubalen sauyin yanayi da muke fuskanta ko yaushe a wannan tsibiri namu wanda ke barazana ga samar da abinci."

A yanzu Rashid na aiki tare da kungiyoyin kasa da kasa irin su USAID don horar da matasan Zanzibar wannan nau'i na noman zamani.

"Na horar da kusan matasa 70, da suke da shekaru daga 15 zuwa 35, ba wai wannan tsarin noma kawai ba, har ma da wasu tsare-tsaren daban."

A 2022, an baiwa Rashid kambin 'Ciyar da Makomar Tanzania' karkashin USAID saboda tasirin da yake da shi wajen habaka noman zamani a matakin yankuna.

Ya karkare da cewa "Har yanzu ban gama kammala samun nasarar aikina ba, akwai abubuwa da dama da ya kamata a yi.

"Dole Afirka ta ci gaba da neman sabbin hanyoyi na magance kalubalen samar da abinci a nahiyar, kuma wannan salon noma ba tare da kasa ba na daya daga cikin wadannan hanyoyi."

TRT Afrika