Shatta Wale ya shafe tsawon shekaru 10 na yana harkar sana'ar waka. Hoto: Shata Wale  

Tauraron mawaƙi ɗan asalin kasar Ghana, Charles Nii Armah Mensah Jr wanɗa masoyansa suka fi sani da Shatta Wale, ya ce ya fuskanci matsalar damuwa tun yana yaro bayan mutuwar auren iyayensa.

A wani shirin kai tsaye na Facebook da ya yi, Shatta Wale ya bayyana wa mabiyansa sama da mutum miliyan 1.5 cewa mutuwar auren iyayensa ya haifar masa da "matsalar damuwa da rashin kwanciyar hankali" a rayuwarsa.

Tauraron mawaƙin yana da dimbin masoya a fadin Afirka da kewaye inda yake da mabiya sama da mutum miliyan 1.5 a shafin Facebook kadai.

“Lamarin ya yi matukar tasiri a kaina sosai. Tarwatsewar gidanmu ya matukar shafata. A duk lokacin da na yi magana ko na yi ƙorafi a kan hakan, iyayena sukan dauki a matsayin yaro mara kunya, Don haka, na bar su. Na bar gidan. Na gudu daga inda iyayena suke,'' in ji shi.

Fama da matsalar damuwa

Tauraron mawaƙin ya kasance cikin yanayi na rashin jin daɗi a yayin da yake ba da labarin ƙuruciyarsa cikin bidiyon kai tsaye na Facebook da ya yi.

“Na kwana a kan titi; Na kwana a gaban shaguna. Na kwana a gidajen mai... Na kuma kwana a kan titunan birnin Adabraka,” in ji shi yayin da yake kokarin fitar da hawaye.

Wale ya ce, ya koyi jure matsaloli da damuwar da ya fuskanta daga kuruciyarsa ta hanyar gujewa duk wani abu da ka iya janyo masa damuwa a rayuwa.

“A sakamakon haka, na fara gujewa duk wata damuwa, ina gudu daga mutanen da za su takura min su zame min damuwa. Daga nan ne na koyi yadda ake yanke mutane don ba na son damuwa.

Yana da mahimmanci ka yanke duk wani da ke son kawo maka rashin kwaciyar hankali a rayuwarku, '' in ji Shatta wale.

Nasarar sana'arsa

Shatta Wale, mai shekaru 38 a duniya, ya samu lambobin yawo da dama a sana'ar da shafe sama da shekaru 10 a kai.

Ya yi fice a irin salon waƙe da rawarsa da kuma kwarjinin kalamansa game da ingancin waƙa da martaninsa ga kakkausan suka da yake sha daga waɗanda ba su yaba aikinsa.

A ranar 18 ga watan Maris, 2018, aka karrama shi da lambar yabo saboda gudunmawar da ya bayar ga salon waƙa ta reggae a Ghana a bikin karrama waƙoƙi karo na 37 na Chicago.

Kazalika ya kafa tarihi a matsayin wanɗa ya fi haɗa masu raye-raye bayan da ya lashe lambobin yawo 11 a shekarar 2019 na '3 Music Awards' daya daga cikin manyan shirye-shiryen ba da lambar yabo a fannin nishadi na Ghana.

TRT Afrika